A yau Laraba, abokan arziki, da abokan aiki, da kuma masoya zasu fara kai gaisuwar karshe da karramawa ga marigayiya mai shari’a ta Kotun Kolin Amurka, Ruth Bader Ginsburg.
Za a kai akwatin gawar Ginsburg ginin kotun kolin Amurka yau Laraba da safe don wani biki na mutane kalilan da za a yi, wanda iyalinta da kuma alkalai abokan aikinta zasu halarta. Daga nan za a ajiye akwatin gawar kan matakalar da ke gaban ginin kotun don jama’a masu zuwa yi mata ganin karshe su je su ganta, har zuwa gobe Alhamis, za a ajiye akwatin ne akan dandamalin katakon da aka kera don akwatin gawar tsohon Shugaban Amurka Abraham Lincoln bayan da aka kashe shi a shekarar 1865.
Haka kuma ranar Juma’a za a sake nuna wa marigayiyar jinjina da karramawa a lokacin da za a kai akwatin gawarta ginin majalisar dokokin Amurka da ke tsallaken titi, inda za a ajiye ta a bangaren da ake ajiye mutum mutumin shahararrun Amurkawa, ita ce zata zama mace ta farko da aka yi wa irin wannan karramawar. Jama’a zasu iya ganin akwatin gawar bayan an yi wani biki da aka gayyaci wasu baki.
Facebook Forum