Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar Guguwar Sally Na Iya Haifar Da Mummunar Ambaliyar Ruwa


Akwai alamar mahaukaciyar guguwar nan ta Sally za ta janyo ambaliyar ruwa idan ta karasa dannowa zuwa gabar teku a yau Laraba a Amurka.

Kwararru a fannin yanayi na gargadin cewa mahaukaciyar guguwar Sally zata haifar da mummnar ambaliyar ruwa yayin da ta ke dosar sassan yankin gabar tekun Gulf na Amurka yau Laraba.

Cibiyar sa ido kan mahaukaciyar guguwa da ake kira NHC a takaice ta ce muguwar guguwar ta sauka yau Laraba da safe a kusa da garuruwan da ke gabar tekun, da Alabama, da ke gabar teku, dauke da iska mai gudun kilomita 165 cikin sa’a daya, abinda ya sa ta zama mahaukaciyar iska a mataki na 2 a ma’aunin guguwa mai matakai 5, zama da muni.

Cibiyar ta NHC ta fidda gargadin mahaukaciyar guguwa ga mazauna yankin iyakokin Missisipi da Alabama zuwa sassan yankin arewacin jihar Florida yayin da mahaukaciyar guguwar Sally ta doshi arewacin yankin. Kwararru a fannin yanayi sun ce yankin zai fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya mai yawan sentimita 20 zuwa 30 tsawon yinin yau, da kuma wasu wurren da ake hasashen za su samu ruwan sama mai yawan sentimita 88, abinda zai haifar da mummunar ambaliyar ruwa ta tarihi.

Haka kuma ana ganin za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a ciki-cikin arewacin yankin zuwa jihohin Virginia da North Carolina da kuma South Carolina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG