An ga hoton wata mota wadda zata iya daukar makami mai linzami samfurin ballistic a filin faretin sojojin Koriya Ta Arewa, a cewar wata hukumar nazari ta Amurka, hujja ta baya-baya da ke nuna cewa ta yiwu Pyongyang ta yi amfani da bikin zagayowar ranar kafa jam’iyyar kwaminisancin kasar da ke tafe don baje kolin fasahar makamai masu linzaminta.
38 North, wani shafin yanar gizo da ke maida hankali kan Koriya Ta Arewa, ya ce wani hoto daga tauraron dan’adam da aka samu a jiya Talata ya nuna wata mota da ta yiwu ta daukar makami mai linzami ce a filin horar da sojojin Mirim da ke wajen birnin Pyongyang, inda koriya Ta Arewar ke gudanar da babban faretin sojojinta.
“Yayin da hotun kadai bai isa ya tantance takamaimai ko wace irin mota ba ce, girmanta da fasalinta na nuna cewa ta yiwu ta daukar babban makami mai linzame ce, a cewar shafin a jiya Talata.”
Hoton ya nuna motar na da tsawon kimanin mita 20 da kuma fadin mita 3, girmar da za ta iya sa motar ta dauki makami mai linzamen ICBM, a cewar sanarwar hukumar nazarin.
Facebook Forum