Amurka za ta ci gaba da taimaka wa Ukraine a kokarin da take yi na kai hatsi kasuwannin da ke matukar bukatarsa ko da ta wasu hanyoyi ne.
Masu sharhi kan lamuran siyasa da diflomasiyya na ganin cewa yunkurin juyin mulkin da aka yi a Nijar sam bai zo da mamaki ba, idan aka yi la'akari da tarihin rikicin siyasar kasar da ke yammacin Afirka.
Dakarun tsaro a Kamaru na neman akalla mutane 25 da 'yan bindiga suka sace a kan iyakar kasar da Najeriya. Al’ummar yankin na kira ga gwamnatoci da su dauki matakan dakatar da kungiyoyin ‘yan bindiga da ke aiki a bangarorin iyakar biyu, a cewar rahoton Moki Edwin Kindzeka wakilin Muryar Amurka.
Ana ci gaba da maida martani game da tuhumar Donald Trump a Amurka inda kawuna suka rabu, wannan dai shi ne karon farko da ake tuhumar wani tsohon shugaba a Amurka.
An yi harbe-harbe a cikin wani gini da ‘yan cocin Jehovah’s Witness suke amfani da shi a birnin Hamburg da ke arewacin Jamus a yammacin jiya Alhamis, kuma mutane da yawa sun mutu wasu kuma sun jikkata, a cewari ‘yan sanda.
Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Farfesa Mahmood Yakubu ta mika shaidar lashe zabe ga zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan kasar Alhassan Ado Doguwa a gaban kotun majistire ta jihar, bisa tuhumar sa da hannu a tarzomar zabe, inda wasu mutane uku suka rasa rayukansu a yankin mazabarsa.
'Yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa a Najeriya sun ce za su kalubalanci sakamakon zaben da ya ayyana dan takarar jam'iyya mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara.
Wasu rumfunan zabe a babban birnin tarayyar Najeriya sun kasance da dogayen layuka har cikin daren Asabar yayin da masu kada kuri'a su ke jira don su kada kuru'unsu.
Wasu na kallon babban zaben bana a matsayin wanda zai kawo sauyi sosai a Najeriya, kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka kuma mafi karfin tattalin arziki.
An haifi Atiku a 1946 a yankin Jada na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya kuma nemi takarar shugabancin Najeriya sau biyar in an hada da zaben nan na 2023 inda ya ci nasarar samun tikiti sau uku.
Da safiyar ranar Laraba an tashi da jin karar manyan bindigogi a garin Jema da ke cikin karamar hukumar mulkin Illela ta jihar Sokoto wanda ya hada iyaka da Nijar, a cewar mazauna garin.
A wurin taron majalisar tsaro ta Najeriya, masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro sun tabbatar wa shugaba Muhammadu Buhari cewa a shirye suke su samar da tsaro a zaben da za a yi a kasar a karshen mako.
Ofishin hukumar zaben Najeriya da ke Dutse fadar gwamnatin jihar Jigawa, ya ce ya fara rarraba kayayyakin zabe zuwa kananan hukumomi da mazabu na sassan jihar, a wani mataki na tunkarar zaben ranar Asabar mai zuwa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta maida martani kan zargin da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa'i ya yi na cewa wadansu hadiman gwamnati a fadar shugaban kasa suna yi wa jam'iyyar zagon kasa don hana ta samun nasara a zaben da ke tafe.
Rahoton da babban bankin Najeriya ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya ce bankin ya kashe dalar Amurka biliyan 11.42 a cikin watanni 7, daga watan Janairu zuwa watan Yuli na shekarar 2022 domin a farfado da darajar naira.
Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya na binciken gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele bisa zargin aikata laifukan da suka shafi kudi, da tallafa wa ayyukan ta’addanci, da kuma yin almundahana.
Wata kotun tarayya da ke West Virginia a Amurka ta samu wani dan Najeriya mai suna Ayodele Arasokun da laifin damfarar gwamnatin Amurka dala miliyan 60 ta hanyar shigar da bayanan haraji na karya.
Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labor Datti Baba Ahmed ya bayyana goyon bayansa kan bukatun malaman makarantar jami’a da ke yajin aiki a Najeriya sama da wata shida kenan.
Domin Kari