NIAMEY, NIGER —
A shirin da ya gabata an ji yadda kungiyoyin masu bukata ta musamman a Najeriya suka dage da ayyukan fadakar da magoya baya domin shiga al’amuran babban zaben da ake shirin gudanarwa a kasar a ranar 25 ga watan Fabrairun nan ta yadda za su mori romon dimokradiyya.
A yau shirin ya leka jihar Zinder a jamhuriyar Nijar don jin halin da ake ciki game da batun ilimin kurame.
Shekaru sama da 40 bayan kafa makarantun kurame na farko a kasar, bayanai na nunin a na fama da karancin kayan karatu duk da tallafin da ake samu jefi-jefi daga kungiyoyi masu zaman kansu, kamar yadda daraktan makarantar kuramen Zinder ya shaida wa wakiliyar sashen hausa Tamar Abari.