Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 25 A Kusa Da Iyakar Kamaru Da Najeriya


'Yan bindiga a yankin jihar Kebbi
'Yan bindiga a yankin jihar Kebbi

Dakarun tsaro a Kamaru na neman akalla mutane 25 da 'yan bindiga suka sace a kan iyakar kasar da Najeriya. Al’ummar yankin na kira ga gwamnatoci da su dauki matakan dakatar da kungiyoyin ‘yan bindiga da ke aiki a bangarorin iyakar biyu, a cewar rahoton Moki Edwin Kindzeka wakilin Muryar Amurka.

Jami’ai a Kamaru sun ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mutanen ne a lokacin wasu hare-hare da ake kai wa a duk rana a wannan makon a gundumar Ako da ke kan iyakar kasar da Najeriya daga yamma.

Jami’an gundumar sun ce mazauna kauyukan da dama sun tsere daga hare-haren.

Magajin garin Ako, Nkanya Nkwai, ya ce ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, na kai farmaki a bangaren iyakar Kamaru da Najeriya.

“Ya zuwa yanzu mutane 25 aka yi garkuwa da su, muna fargabar ta yiwu adadin wadanda aka yi garkuwa da su ya zarta haka, saboda tun daga ranar Litinin ba mu iya magana da mutanen da ke bakin iyakar Buku, da Abafum, da Akwancha da ke Najeriya ba kuma babu wani sako daga masu garkuwa da mutanen domin su sanar da mu dalilin da ya sa suke yin haka. Ba mu sani ba ko wadanda aka sace suna raye ko an kashe su," cewar Nkwai.

Rundunar sojan Kamaru ta ce ta tura sojoji a kan iyakar kasar da Najeriya domin ceto wadanda aka sace tare da dakile 'yan bindigar.

Kungiyar raya al'adu ta Mbembe, kungiyar agaji ce ta kasar Kamaru da ke taimaka wa kauyukan da ke kan iyaka da Najeriya.

Shugaban kungiyar Abel Shewa, ya ce mahara na ci gaba da korar mazauna kauyukan yankin a kullum, kuma galibinsu mata ne da yara.
“Babu mutane a yawancin kauyukan yayin da mazaunansu suka tsere zuwa Najeriya da kuma garin Ako domin tsira, a saboda haka muna rokon kungiyoyin agaji da su kawo dauki, su zo don su taimaka wa mutanen da suka rasa muhallansu kuma yanzu ba su da wani abu. Mata da yara suna shan wahala, kuma lamarin ya shafi gaba dayan farar hula, sannan kuma mutane na zama cikin fargaba,” a cewar Shewa.

Shewa ya yi kira ga gwamnatin Kamaru da ta samar da agaji ga ‘yan gudun hijirar sannan ya roki mazauna garuruwan da suka sauke su da su tallafa musu da abinci da matsugunni.

Jami’an yankin sun shaida wa Muryar Amurka cewa suna kyautata zato Fulani ne masu satar mutanen daga Najeriya.

Jami’an sun ce lokuta-lokuta makiyayan kan tsallaka cikin Kamaru da shanunsu domin yin kiwo, lamarin da ke haddasa rikici da manoma. Hakazalika, kauyukan da ke kan iyaka da Kamaru su ma sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga daga Najeriya, kamar mayakan Boko Haram.

Amma wannan shi ne karon farko cikin sama da shekara goma da jami'ai ke zargin Fulani makiyaya da kai wani gagarumin farmaki.

Sojojin Kamaru sun kafa wani shingen bakin iyaka a kauyen Baoro a shekarar 2012 bayan wani rikici da ya barke tsakanin Fulani makiyaya daga Najeriya da manoman Kamaru a kan mallakar filaye.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG