Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: Hukumar INEC A Jigawa Ta Ce Ta Shirya Tsaf Don Zabe


Zaben 2023
Zaben 2023

Ofishin hukumar zaben Najeriya da ke Dutse fadar gwamnatin jihar Jigawa, ya ce ya fara rarraba kayayyakin zabe zuwa kananan hukumomi da mazabu na sassan jihar, a wani mataki na tunkarar zaben ranar Asabar mai zuwa.

Hukumar INEC a jihar Jigawa ta ce yanzu haka kusan dukkan kayayyakin zabe sun kai ga shalkwatar kananannan hukumomin jihar 27, in banda takardun rubuta sakamakon zabe da na’urar BVAS ta tantance masu kada kuri’a.

Kakakin ofishin hukumar a Dutse, Mr John Kaiwa, ya ce kwamishinan zabe na jihar tare da kusoshin hukumar na ci gaba da ganawa da kungiyoyin sanya ido na ciki da wajen Najeriya.

Mr. Kaiwa ya kuma ce tuni aka kammala bada horon da ya kamata ga ma’aikatan da hukumar INEC ta dauka domin gudanar da aikin zabe a sassan jihar.

Zaben 2023 audio
Zaben 2023 audio

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ke kalubalantar Rabiu Musa Kwankwaso da ke takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP. Yace sun shirya tsaf domin tunkarar zaben ranar Asabar kuma ya na da yakinin samun nasara akan dantakarar ta NNPP.

Yanzu haka dai gamayyar kungiyoyin Malaman addinin musulinci a Kano sun gudanar da wani taro na musamman domin cimma matsaya dangane da zaben da za’ a yi a ranar Asabar mai zuwa.

Malam Abba Adam Koki, wanda ya jagoranci taron gamayyar kungiyoyin Malaman addinin Islama a Kano ya ce gamayyar kungiyoyin da suka hada da Izala, da Tijjaniya, da Kadiriyya, da sauran kungiyoyi sun cimma matsaya kan amincewa a zabi Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
XS
SM
MD
LG