Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ta ASUU ta tsawaita yajin aikin da ta fara watanni 3 da suka gabata zuwa watan Agusta, bisa dalilai masu alaka da halin ko-in-kula da ta ce gwamnatin Najeriya na nunawa.
Wani bene mai hawa uku, wanda iyalai ke ciki, ya rushe a babban birnin hada hadar kasuwancin Najeriya na Legas, inda mutane 8 suka mutu wasu su 23 kuma suka jikkata, wadanda aka kai su asibiti, a cewar hukumar kai daukin gaggawa a yau Litinin.
Hukumar ta dauki wannan matakin ne bayan wani hargitsi da aka samu a lokacin da Najeriya ta kara da Ghana a wasan neman shiga gasar kwallon ƙafa ta duniya a watan Maris.
A Najeriya, kwararru a fannin shari'a sun mayar da martani akan matakin da Majalisar Dattawa ta dauka na amincewa da kafa karin cibiyoyin horrar da lauyoyi 6 a kasar. A yayin da wasu ke yabawa da yin haka, wasu na cewa siyasa ce kawai.
Wata sanarwa daga rundunar sojan Najeriya ta ce ta kai farmaki a wasu wuraren mayakan Boko Haram a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, ciki har da wata kasuwar mayakan.
Najeriya ta shiga jerin kasashe 12 a fadin duniya da aka samu bulluwar sabon nau’in cutar coronavirus da ake kira Omicron. Nau’in cutar da aka gano a kudancin nahiyar Afrika ya shigo Najeriya ne ta hanyar wasu matafiya biyu da suka zo kasar daga Afrika ta kudu.
Wanda ya kirkiro kamfanin Tuwita (Twitter), Jack Dorsey ya ce ya ajiye mukaminsa na shugaban kamfanin sada zumuncin Twitter.
Konturolan gidan yarin jIhar Filato, Samuel Aguda yace fursunoni bakwai ne aka kashe a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a gidan yarin a jiya Lahadi.
A yayin da a yau Litinin wa’adin da hukumomi suka dibar wa likitoci da daliban makarantun likitanci ke cika domin yin alllurar rigakafin cutar corona, kungiyar kananan likitoci ta SUSAS da kungiyar daliban dake karantar fannin lafiya a jami’ar AbdoulMoumouni sun yi watsi da wannan mataki.
Duk da kokarin da hukumomi a Najeriya da Amurka ke yi na kame da kuma dakile ayyukan 'yan danfarar kudin Banki da aka fi sani da 419 ko yahoo Yahoo a Najeriya, har yanzu wasu 'yan Najeriya, musanman matasa, na ci gaba da gudanar da wannan muguwar sana'ar ta hanyoyi da dama.
Wasu Masana harkokin tsaro sun jingina adadi mafi rinjaye da aka samu na hare-haren 'yan bindiga a jihar Kaduna da irin matsayin da gwamnatin jihar ke kai na cewa babu sulhu tsakanin gwamnati da 'yan bindiga.
Ziyarar Firai Ministar Denmark Mette Frederiksen ita ce ta farko a Ghana. Wannan ziyarar ta karrama cika shekaru sittin da huldar diflomasiya tsakanin Denmark da Ghana ce. ‘Yan kasar Denmark na ganin kasar Ghana a matsayin muhimmiyar kawar kawance a Afrika ta yamma da baki dayan Afrika.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun bayyana shirin cimma yarjejeniyar odar jiragen yaki da motoci masu sulke daga kasar Turkiya da nufin karfafa wa dakarun kasar gwiwa a yakin da suke kafsawa da ‘yan ta’adda.
A cikin shirin wannan makon a birnin Jos dake arewacin Najeriya, za ku ga yadda kasuwa ta budewa wasu matasa masu kirkire-kirkire da suke sarrafa itace wajen yin cokula da sauran abubuwan kicin, da wasu rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon mazuna birnin Jos a arewacin Najeriya su na ci gaba da fama da matsalar karancin ruwa, lamarin da ke sa wasu masu sana’o’i amfani da ruwa mara tsafta wajen wanke-wanke da sauran al’amura, da wasu rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon, kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières ta yi kiran daukan matakin gaggawa don shawo kan barkewar cutar kyanda a jihar Bornon Najeriya, da wasu rahotanni.
A cikin shirin wannan makon hukumomin Najeriya na kara kokari wajen yi wa mutane da yawa rigakafin COVID-19 bayan da aka sami tsaiko wajen yin rigakafin saboda wasu bayanan karya, da wasu sauran rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon hukumomin lafiya a jamhuriyar Nijar sun fara aikin rigakafin cutar Coronavirus, bayan China ta taimaka ma kasar da magungunan rigakafin, da wasu sauran rahotanni.
A cikin shirin na wannan makon wasu mata matasa a jihar Sokoton Najeriya su na jan hankalin jama’a bayan da suka rungumi sana’ar gyaran mota, wacce aka san maza ne da ita a wannan yanki na kasar, da wasu sauran rahotanni.
Domin Kari