A ranar Laraba ne shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro na kasa, yayin da ya rage ‘yan kwanaki a gudanar da babban zaben kasar ranar 25 ga watan Fabrairu.
Taron dai ya samu halartar shugabannin hukumomin tsaro, ministan sharia, da sauran masu ruwa da tsaki a fannin tsaron kasar.
Bayan taron Ministan shari’a kuma babban alkalin Najeriya Abubakar Malami, ya bayyana cewa harkokin zabe na bukatar kulawa ta bangaren tsaro, dalili kenan ya sa aka gayyaci hukumomin tsaro don su yi bayani kan shirye-shiryen da suka yi.
Ya kuma ce hukumomin sun bada tabbacin cewa sun dauki duk matakan da suka dace domin tabbatar da an yi zaben cikin lafiya, sun kuma gamsu da shirye-shiryen hukumomin tsaron.
Babban Sufetan ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali, ya bayyana cewa za a girke jami’an tsaro a rumfunan zabe don su tabbatar da an yi aikin zaben cikin lumana, bayan haka an tanadi jami’an tsaron da zasu yi sintiri tare da tabbatar da tsaro, shi ya sa aka takaita zirga-zirga a lokacin zaben a cewarsa.
Saurari rahoton Umar Faruk Musa: