Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masharhanta Sun Ce Ba Lallai Juyin Mulkin Da Sojoji Suka Yi A Nijar Ya Dore Ba


Niger Tensions
Niger Tensions

Masu sharhi kan lamuran siyasa da diflomasiyya na ganin cewa yunkurin juyin mulkin da aka yi a Nijar sam bai zo da mamaki ba, idan aka yi la'akari da tarihin rikicin siyasar kasar da ke yammacin Afirka.

WASHINGTON, DC - An yi juyin mulki har sau hudu bayan yunkurin juyin da aka yi koluta da yawa da basu yi nasara ba tun bayan da Nijar ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960. Sai dai masu sharhi na ganin cewa saboda kasancewar shugaba Mohamed Bazoum daga tsirarun kabilun Jamhuriyar Nijar kuma an zabe shi ne a karkashin jam’iyyar da ke neman kawo sauye-sauye da yawa, tayiwu hakan ya sa ya fuskanci turjiya daga sauran kabilun da suka fi rinjaye.

A jawabin da suka yi wa al’umar kasar, shugaban kwamitin sojan da suka yi juyin mulkin Kanar Amadou Abdramane, ya ce jami'an tsaro sun kifar da gwamnatin ne saboda rashin shugabanci nagari da kuma matsalar tsaro a Nijar. An dakatar da duk wasu harkokin jam'iyyun siyasa a kasar a ranar Alhamis har sai yadda hali ya yi, a cewar Abdramane ta talabijin din kasar.

Sojojin CNSP da suka yi juyin mulki a Nijer
Sojojin CNSP da suka yi juyin mulki a Nijer

Abdourahmane Alkassoum, wani mai sharhi kan harkokin siyasa da tsaro a yankin kudu da hamadar Sahara, ya fada wa Muryar Amurka cewa kusan har yanzu akwai rudani a Yamai babban birnin kasar, kwana daya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

"A halin yanzu babu jama’a sosai a tsakiyar birnin saboda fargabar ba a san me zai taso ba. Muna cikin yanayin rudani, inda a wani bangaren alamu ke nuna juyin mulkin ya tabbata, a daya bangaren kuma wasu ke ganin bai yi nasara ba," a cewar Alkassoum.

A watan Afrilun 2021 ne dai zababben shugaban kasa Mohamed Bazoum ya sha rantsuwar kama aiki.

Dr. Edgar Githua, kwararre kan harkokin huldar kasashe da kuma diflomasiyya a jami'ar kasa da kasa ta Amurka da ke birnin Nairobi, ya fada wa Muryar Amurka cewa rikicin siyasar da ya faru a baya-bayan nan bai zo da mamaki ba.

Nijar kasa ce da ta fuskanci juyin mulki har sau hudu a tarihinta, a saboda haka al’adar siyasar kasar ita ce sojoji na ganin suna da ikon yin abinda suke so ko kuma an basu damar ganin akwai bukatar su taka rawa a siyasar kasar,” a cewar Githua.

Rikicin siyasar Nijar
Rikicin siyasar Nijar

Githua ya kuma ce ta yiwu batun kabilar da Shugaba Bazoum ya fito shi ma wani dalili ne na yunkurin juyin mulkin.

“Shi balarabe ne daga Diffa, daga tsirarun kabilun kasar. Ya zo ya kawo sauye-sauye sosai saboda ya gaji mulkin kasa mai kabilu masu rinjaye, kamar Hausawa, Zabarmawa, Abzinawa. Abinda ke faruwa da irin wadannan shugabannin da suka gaji mazabu da yawa inda su kuma suka fito daga tsiraru, sai su ji kamar an yi musu kawanya saboda sauran mutanen da ke da fada a ji a gwamnati daga kabilu masu rinjaye suka fito, wadanda ke ganin ko suka yi imanin cewa baka cancanci shugabantar su ba," a cewar Githua.

Kungiyar raya kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, da kungiyar Tarayyar Afirka, da sauran kasashen duniya sun yi Allah wadai da abubuwan da ke faruwa a Nijar tare da yin kira da a gaggauta sakin shugaban ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban Nijar Mohamed Bazoum
Shugaban Nijar Mohamed Bazoum

A yankin da a baya-bayan ya yi ta fuskantar juyin mulki a kasashen Mali, Burkina Faso da Guinea, Nijar ta ci gaba da bin tsarin dimokradiyya tun bayan da Bazoum ya hau karagar mulki.

Kasar Nijar, da ke yankin kudu da sahara ta sha fama da rikicin masu kaifin kishin addinin Islama, kuma Faransa da ke taimakawa a yakin na da sojoji kusan 1,500 a cikin kasar.

Githua yace baya tunanin wannan yunkurin juyin mulkin zai yi nasara.

“Kungiyar Tarayyar Turai, Amurka da Faransa ba za su bar Nijar ta fadi ba, saboda sun yi imanin cewa Nijar na da muhimmnci a yankin wajen dakile ‘yan tawaye, ta'addanci, da ayyukan Al Qaeda, Boko Haram da makamantansu. Tuni dama Amurka ta girke sojoji na musamman kusan 1,000 a Nijar, haka ita ma Faransa tana da su da yawa,” a cewar Githua.

Zanga-zangar magoya bayan Bazoum a Yamai.
Zanga-zangar magoya bayan Bazoum a Yamai.

A ranar Laraba Magoya bayan Bazoum sun taru a gaban ginin majalisar dokokin kasar domin yin kira da a sake shi. Amma a ranar Alhamis, wasu kuma sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan juyin mulkin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG