A ranar Laraba ne Farfesa Yakubu ya mika takardar shaidar ga Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima.
Tinubu ya gayyaci wadanda ya yi takara da su amma ba su samu nasara su ba da goyon baya a yi aiki tare don ci gaban kasa.
Zababben shugaban wanda a kaikaice ke nuna mulki ba abu ne da zai dauwama ba, ya bayyana cewa nan gaba matasa masu karancin shekaru da mata zasu zo su karbi irin wannan shaida.
Wakilan jam’iyyu da suka amince da sakamakon zaben irinsu Muhammad Lawan Nalado, na cewa ba za a yi nadamar zuwan Tinubu karagar mulki ba.
Sama’ila Sifawa, na daga cikin wadanda suka yi aikin sa ido kan zaben, ya na mai cewa in an ga ‘yan uwa ko yarbawa da yawa a gwamnatin ba sabon abu ba ne.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da wasu gwamnoni na daga cikin wadanda su ka shaidar karbar takardar shaidar.
An so a yi turereniyar jama’a a wajen shiga dakin taron inda wasu mutane suka fadi har kasa, yayin da ‘yan sane suka yi wuf suka sace wayar salula ta Sanata Kabiru gaya.
Saurari rahoton: