Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martani Game Da Tuhumar Trump Na Nuna Rabuwar Kawuna Sosai A Amurka


Tsohon shugaban Amurka Donald Trump
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump

Ana ci gaba da maida martani game da tuhumar Donald Trump a Amurka inda kawuna suka rabu, wannan dai shi ne karon farko da ake tuhumar wani tsohon shugaba a Amurka.

'Yan jam'iyyar Republican ta Trump sun caccaki mai gabatar da kara bisa ikirarin da suka yi na cewa bita da kullin siyasa ne kawai, yayin da 'yan jam'iyyar Democrat suka ce babu wanda ya fi karfin doka.

Hatta ‘yan Republican da ke so su fafata da Trump wajen neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Republican a 2024, sun fito don kare shi bayan da wani babban alkali a birnin New York ya gabatar da tuhuma kan Trump bisa zarge-zargen da ake yi masa masu alaka da biyan wata ‘yar fina-finan batsa dala 130,000 a matsayin na toshiyar baki a shekarar 2016, kan ikirarin da ta yi na cewa Trump ya neme ta shekaru goma a baya.

Trump dai ya dade da musanta ikirarin na tauraruwa, Stormy Daniels.

Stormy Daniels
Stormy Daniels

Gwamnan jihar Florida Ron DeSantis, wanda bai sanar da aniyyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2024 ba, amma ya zo na biyu a ra’ayoyin jama’a kan neman takarar shugaban kasa na jam'iyyar bayan Trump, ta Twitter ya zargi mai gabatar da kara na New York Alvin Bragg, dan jam'iyyar Democrat, da amfani da tsarin doka "don ciyar da wata manufa ta siyasa gaba," abin da ya ce hakan ya saba tsarin doka."

DeSantis ya ce ba zai yi aiki tare da jami'an New York ba don taso keyar Trump daga Florida don fuskantar tuhume-tuhume. Ko da yake, lauyan Trump ya ce tsohon shugaban zai tashi daga Florida zuwa New York don mika kansa.

Donald Trump
Donald Trump

A game da tuhumar, Nikki Haley, tsohuwar jakadiyar Trump a Majalisar Dinkin Duniya wacce ta sanar da aniyyar tsayawa takarar shugaban kasa a 2024, ta ce tamkar ramuwar gaya ne ba adalci ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG