Yayinda binciken jin ra'ayoyin jama'a ya nuna cewa kashi 30 na al'ummar Venezuela sau daya suke cin abinci a rana, sai ga shugaba Maduro na ragargazar nama a wani gidan cin abinci mai tsada.
Kasashen biyu sun sha kokarin karfafa dangantakar tsaro da siyasa tsakaninsu.
Sakataren harkokin tsaron Amurka Jim Mattis ne ya bayyana cewa kokarin da ake yi na maido da zaman lafiya a Afghanistan na samun ci gaba.
Shugaban Amurka Donald Trump na ikirarin cewa labarai da abubuwan da aka fada cikin wani sabon littafi da aka rubuta akan shugabacinsa an yi su ne bisa karairayi, don a yaudari jama’a.
A yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana a babbar jam’iyar APC mai mulki a Najeriya game da batun amfani da zaben 'yar tinke ko kato ya bi bayan kato a zaben fidda 'yan takara, yanzu haka shugabanin jam’iyya na jihohi sun marawa gwamnoni baya.
A daren jiya lahadi ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe mutane sama da 10 a kudancin birnin Jos da ke jihar Filato.
Hukumomi a Najeriya sun hana tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yin taron siyasa a dandalin Eagle Square dake birnin tarayya Abuja.
Gwamnatin tarayyar kasar na dab da kammala gyare-gyare akan hanyar Okigwe ta Arondizuogu zuwa garin Akokwa wacce ta dade da lalacewa, da nufin bunkasa kasuwanci a fadin yankin kudu-maso-gabashin Najeriya,
Gwamnatin kasar ta amince da yi masu afuwar ne bayan da suka rubuta wasikar neman gafara akan abin da suka yi.
Firayin minista Theresa May na wannan ziyarar ne da wakilan ma’aikatun gwamnatin Burtaniyya da kuma wasu daga bangaren kasuwanci kasar dabam dabam.
Ranar Lahadi za a yi jana’izar marigayi Sanata John McCain a kwalejin sojojin ruwan Amurka dake Annapolis, jihar Maryland.
Ranar 23 ga watan Augustan kowacce shekara rana ce da hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da kawo karshen cinikin bayi da akayi shekaru aru aru da suka gabata. Muhimmancin wannan rana shine nuna illar cinikin bayi da kuma hana aukuwar sa a nan gaba.
Kwararru na kokarin yin Fasahun da zasu taimaka wajen kiyaye lafiyar jarirai a yankunan Afrika.
Kungiyar Myetti Allah ta Fulani makiyaya a Najeriya ta nesanta kanta da wa’adin da aka ce ta baiwa shugaban majalisar dattawan Najeriya Dr. Abubakar Bukola Saraki na ya yi murabus ko ta tilasta masa yin murabus.
Yau kotun kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe zata fara sauraron karar da jam’iyyar hamayya ta shigar tana kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar watan da ya gabata.
'Yar majalisar ta na kuma neman hukumar tara harajin Amurka ta bayyana harajin 'Yan takara.
Kalubalen siyasar shugaban Amurka Donald Trump ya karu yau Talata bayan da tsohon manajan yakin neman zaben sa, Paul Manafort ke fuskantar hukuncin zuwa gidan yari.
'Yan Jam'iyyar Republican na nuna damuwa akan ra'ayoyin jama'a game da farin jinin shugaban Amurka Donald Trump.
Mayakan kungiyar Taliban dake Afghanistan sun ce ba su suka kai hare hare a Kabul ba.
Hukumomin kiwon lafiyar al’ummar a Janhuriyar Nijer sun bada sanarwar mutuwar mutane 26 daga cikin mutane kusan 1500 da suka kamu da cutar amai da gudawa a gundumar Madarunfa dake yankin Maradi.
Domin Kari