Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Myetti Allah Tace Bata Shiga Harkokin Siyasar Najeriya


Kungiyar Myetti Allah ta Fulani makiyaya a Najeriya ta nesanta kanta da wa’adin da aka ce ta baiwa shugaban majalisar dattawan Najeriya Dr. Abubakar Bukola Saraki na ya yi murabus ko ta tilasta masa yin murabus.

Sakataren kungiyar na Kasa, Baba Usman Ngelzarma ya shaidawa sashen Hausa na Muryar Amurka cewa sun sami labarin cikin kaduwa, kuma tuni suka kaddamar da bincike akan maganar, da wani mai suna Garus Gololo ya yi da sunansu, yace muddin suka tabbatar da hakan to zasu dauki mataki akansa.

Baba Usman Ngelzarma ya nesanta kungiyar Myetti Allah da shiga harkar siyasa ta kowacce siga, kana yace, Garus Gololo da aka ce ya bada wa'adin a madadin Myetti Allah, shi ba kowa bane a kungiyar don haka ba shi da hurumin Magana da yawunsu.

Babban sakataren Myetti Allah ya ce an kafa kungiyarsu ne da zummar kare muradin Fulani makiyaya, kuma ba ruwan kungiyar da duk wata harkar siyasa.

A nasa bangaren, Garus Gololo da aka ce ya fidda sanarwar, ya ce shi babban jami'i ne a kungiyar Myetti Allah ta kasa, amma ba da yawun kungiyar ya bada sanarwar ba. Ya kuma shaidawa muryar Amurka cewa ya bada sanarwar ne a madadin sa na Uban kungiyar Fulani Yan Jam'iyyar APC na Najeriya.

Gololo ya kara da cewa, a matsayinsa na dan jam’iyyar APC yana da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa duba da yadda Bukola Saraki ya fice daga Jam'iyyar, don haka ya kamata ya sauka daga kujerarsa don wani dan APC ya maye gurbinsa.

Garus Gololo ya zargi Bukola Saraki da jan kafa wajen tabbatar da majalisar ta yi aiki akan kasafin kudi da ma wasu hidindimu da suka shafi kasa da ci gabanta.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG