Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Littafi Ya Bayyana Shugaba Trump a Matsayin "Kidahumi"


Donald Trump, shugaban Amurka
Donald Trump, shugaban Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump na ikirarin cewa labarai da abubuwan da aka fada cikin wani sabon littafi da aka rubuta akan shugabacinsa an yi su ne bisa karairayi, don a yaudari jama’a.

Wasu abubuwa daga cikin littafin akan shugabancin Trump, da wani dan jarida da aka ce ya taimaka wajen kawas da Richard Nixon daga kujerar mulki, ya bayyana gwamnatin Trump a matsayin wadda ke fuskantar juyin mulki da rashin kwanciyar hankali a cikin watanni 19 da kafa gwamnatinsa.

Littafin mai suna Fear: Trump in the White House, mai shafi 448 wanda Bob Woodward ke shirin fiddawa ranar 11 ga watan nan na Satumba, ya bayyana yadda hadimai ke kwashe takardu daga teburin Trump da kuma yin wasu abubuwa da suka kaucewa kudurorin shugaban. Littafin ya kuma bayyana Trump a matsayin “kidahumi” akan lamuran dake faruwa a duniya kuma fadarsa ba ta aiki yadda ya kamata, sannan kuma cike take da rigingimu kala-kala.

Kodayake ‘yan jarida da tsofaffin ma’aikatan fadar White House sun taba bayyana kwamacalar da ta dabaidaye fadar a baya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG