Firayin ministar kasar Burtaniyya Theresa May ta isa Afrika ta kudu yau Talata, kasa ta farko da ta fara yada zango cikin kasashe 3 da zata kai ziyara, da zummar karfafa dangantakar cinikayya bayan ficewar Burtaniyya daga tarayyar Turai.
May ta fadawa wadanda suka taru a birnin Cape Town cewa Burtaniyya na so ta karfafa muradan kasa da kuma dangantakar cinikayya a nahiyar.
Ms. May ta kuma ce, tana so ta kulla kawancen kasuwanci tsakanin Burtaniyya da kasashe kawayenta dake Africa. Dangantakar da zata kawo cigaba da kuma tsaron kasa.
Firayin ministar zata gana da shugabannin Nigeria gobe Laraba kafin ta kammala ziyararta a Kenya ranar Alhamis.
Facebook Forum