Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Sukar Lamiri Sun Caccaki Shugaban Venezuela Akan Cin Abinci Mai Tsada Yayinda Al'umar kasar suke Tagayyara.


Yayinda binciken jin ra'ayoyin jama'a ya nuna cewa kashi 30 na al'ummar Venezuela sau daya suke cin abinci a rana, sai ga shugaba Maduro na ragargazar nama a wani gidan cin abinci mai tsada.

Wani hoton bidiyon da ya nuna shugaban Venezuela Nicolas Maduro yana ragargazar gasasshen nama a wani gidan saida abince mai tsadar gaske ya janyo cece-kuce a fadin duniya a madadin al’ummar kasarsa da talauci ya yiwa katutu.

Wani hoton bidiyon ya nuna wani gwanin dafa abinci Nusret Gokce, wanda kuma ake kira Salt Bae,” yana yankawa shugaban da matarsa Cilia Flores tsokokin nama, a gidan cin abinci Nusret a Istanbul, inda duk wata katafariyar tsokar nama ake saida ta akan kudi masu yawa.

Sanatan jihar Florida ta nan Amurka, Marco Rubio ya caccaki mai dafa abincin wanda aka dauki hoton bidiyonsa da shugaban mai mulkin kama karyar na Venezuela,” inda aka nuna shi yana cin abinci mai tsadar gaske, yana kuma busa sigari mai tsada yayinda yunwa ke neman hallaka mutanen Venezuela.”

Rubio ya fadawa jaridar Miami Herald jiya Talata cewa “abin tur ne, wannan mutumin da sanadiyarsa mutane ke fama da yunwa amma ga shi Salt Bae na nuna shi kamar wani jarumi, abin ya bata mani rai.”

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG