Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gabatar da Kudurin Hana Kamun Kafa A Majalisar Dokokin Amurka


'Yar majalisar ta na kuma neman hukumar tara harajin Amurka ta bayyana harajin 'Yan takara.

Wata ‘yar majalisar dattawan Amurka Elizabeth Warren ta gabatar da kudurin da zai yi garambawul a dokokin yaki da ayyukan cin hanci da karbar rashawa a gwamnatin kasar, wanda zai zo da sabbin matakan da za su takaita yin kamun kafa wajen wasu jami’an gwamnati, da wasu dokoki da za su kiyaye harkokin ajiyar kudaden jami’ai, da kuma matakan tabbatar da an yi gaskiya da adalci da zummar bayyanawa jama’a yadda ake fitowa da tsare-tsaren manufofin kasa.

A lokacinda take maganar a cibiyar ‘yan jaridun Amurka dake nan Washington jiya Talata, ‘Yar majalisar daga jihar Massachusetts ta ce canje-canjen za su magance abinda ta kira “abubuwa mafi muni da ba a sani ba akan yadda ake amfani da kudi wajen sarrafa harkokin gwamnatin Amurka”.

Daya daga cikin abubuwan da kudurin ya kunsa shine neman hukumar tara harajin kasar da ake kira IRS a takaice, ta rinka fidda bayannan harajin shugaban kasa, da mataimakinsa, da na ‘yan majalissa, da kuma na kamfanoni ko kungiyoyin da ba na neman riba ba, da ‘yan takarar suka mallaka. Kuma duk mai son zama shugaban kasa ko mataimakinsa, dole ne ya bada bayanin harajinsa na shekaru 8 baya.

A yanzu haka ba a fidda wadannan takardun ba kuma an hana hukumar harajin kasar fidda su ga jama’a.

A lokacin yakin neman zaben shekarar 2016, shugaba Donald Trump dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican a wancan lokacin bai bada bayannan harajinsa ba. Amma abokiyar takararsa ta jam’iyyar Democrat, Hilary Clinton a wancan lokacin ta bada na ta takardun harajin daga shekarar 2007-2015.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG