Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Jami'an Amurka da na India Zasu Gana Akan Rasha


Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen Amurka
Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen Amurka

Kasashen biyu sun sha kokarin karfafa dangantakar tsaro da siyasa tsakaninsu.

Matsin lambar Amurka akan India na ta dakatarda sayen mai Rasha makamai daga Rasha, kasar da India ke dauka a matsayin kawa a yankin Wannan batun na cikin muhimman batutuwa da za a tattauna akai a yayinda India da Amurka ke shirin yin muhimmin taron tuntubar juna da zummar karfafa dangantakar siyasa da dabaru.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da sakataren tsaron Amurka Jim Mattis za su gana da takwarorin aikinsu, wato ministar harkokin wajen India Sushma Suwaraj da kuma ministan tsaro Nirmala Sitharaman a birnin New Delhi gobe Alhamis.

Ganawar, wadda aka dage har sau biyu a baya, na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin karfafa dangantaka yayinda kasashen ke kokarin daukar matakan samun daidaito da China.

Wani batun kuma da za’a tabo a goben shi ne karfafa wata yarjejeniya wadda za ta ba India damar shiga tsarin fasahar zamani na yin makamai da kuma ba dakarun damar yin musayar bayanai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG