A yau Laraba ne tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya shirya yin taron ayyana tsayawa takara a dandalin Eagle Square dake Abuja, amma hukumar dake kula da wuri ta hana shi bisa wasu dalilai.
A wata hira ta musamman da sashen hausa na muryar Amurka yayi da shi, Sanata Kwankwaso ya fadi cewa, kammar yadda suka kaddamar da yakin neman zabe a shekarar 2015 a Abuja wannan karon ma haka suka tsara, bayan sun nemi iznin a basu wurin, an kuma amince har sun biya kudi.
"Ana gobe taron, wato jiya Talata kenan, sai ga sako ta hanyar ‘yan sanda cewa ba za mu iya amfani da wurin ba, bayan haka aka kuma hana mu amfani da wani filin fareti duk a cikin birnin Abuja, a cewar Kwankwaso."
Sanatan ya cigaba da cewa, a saboda haka suka nemi wani wuri cikin gaggawa don yin taron tunda jama’a sun riga sun fito daga wurare dabam dabam. Kuma, a cewarsa, an yi taro an gama lafiya.
Wasu bayanai na nuna cewa zuwan Firayin ministar kasar Burtaniyya Theresa May ne ya sa aka hana Sanatan gudanar da taronsa. Amma a nasa bayanin ya ce "wanna zancen hira ce" domin babu abinda ya hada biri da gada. Ya kuma ce idan ma an ce haka, ai Ms. May ma za ta yi murna saboda irin wannan taron na nuna cigaban dimokradiyya, amma matakin da aka dauka yana iya ba kasashen yammacin duniya dake muradin dimokradiyya haushi.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa bai kaddamar da taron tsayawa takarar a jihar Kano garin sa na asali ba, sai ya ce ai ko shekaru hudu da suka gabata a lokacin da yake gwamnan jihar Kano a birnin Abuja yayi taron.
Ga hirar da Usman Kabara yayi da Sanata Kwankwaso cikin sauti.
Facebook Forum