Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Wasu Mutane 14 Afuwa a Cambodia


Gwamnatin kasar ta amince da yi masu afuwar ne bayan da suka rubuta wasikar neman gafara akan abin da suka yi.

Kasar Cambodia ta saki wasu mutane su 14 ‘yan jam’iyyar adawar da aka soke a daidai lokacin da aka yi wani zabe mai cike da sarkakiya a kasar da ya kara wa’adin shugabancin Firai minista Hun Sen, wanda ya share sama da shekaru 30 akan kujerar mulkin kasar.

An saki mutanen ne da safiyar yau Talata daga gidan yarin Prey Sar a Phnom Penh bayan da sarkin Cambodia ya nemi ayi masu afuwa. An same su da laifi ne akan wani bore da suka tada bayan da suka yi wata zanga-zanga akan titi da ta rikide ta koma tarzoma. An yanke masu hukuncin zuwa gidan yari tsakanin shekaru 7 zuwa 20.

Mutanen su 14 mambobin jam’iyyar National Rescue Party ne na Cambodia, wadda kotun kolin kasar ta soke a shekarar da ta gabata, don ba jam’iyyar Hun Sen-ta Cambodia’s People’s party damar samun nasarar lashe duka kujerun majalisar 125 a babban zaben kasar da aka yi a watan da ya gabata. Wasu jam’iyyun adawa 19 sun yi zaben, amma adawar su ba tayi karfi ba sosai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG