Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Najeriya da Nijer na Cigaba da Fadakarwa Akan Cutar Cholera


Hukumomin kiwon lafiyar al’ummar a Janhuriyar Nijer sun bada sanarwar mutuwar mutane 26 daga cikin mutane kusan 1500 da suka kamu da cutar amai da gudawa a gundumar Madarunfa dake yankin Maradi.

A yayin ganawarsa da wakilan kafafen kasa da kasa ne ministan kiwon lafiyar al’umma, Dr. Iliyasu Idi Mainasara ya yi bayani game da halin da ake ciki a kauyukan yankin Maradi masu makwaftaka da garin Jibia dake Najeriya, inda a farkon watan jiya aka samu barkewar annobar cutar amai da gudawa da ake kira Cholera da turanci wadda ta janyo asarar rayuka da dama.

Binciken likitoci ya yi nuni da cewa amfani da ruwan gulbi a matsayin ruwan sha a wasu kauyukan Madarunfa ne ya janyo bullar cutar dake bazuwa tamkar wutar daji, a yayin da jama’ar Jibia suka tsinci kansu cikin matsalar ambaliyar ruwa cikin kwanakin baya, saboda haka mahukunta ke jan hankalin al’umma.

Tuni dai hukumomin kiwon lafiyar al’ummar Nijer da na Najeriya suka yanke shawarar hada guiwa da nufin fadakar da jama’a akan riga kafin cutar cholera a garuruwan gundumar Madarunfa da na karamar hukumar mulki ta Jibia.

Ministan kiwon lafiyar Janhuriyar Nijer Dr. Iliyasu Idi Mainasara ya tabbatarda cewa kawo yanzu, babu in da aka samu labarin bullar cutar cholera a sauran yankunan kasar in ban da wasu mutane 3 da aka gano a garin Maradi da ake jinya a asibiti.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG