Shirin Duniyar Amurka na wannan mako, ya yi bitar wasu daga cikin muhimman batutuwna da suka faru a wannan shekarar 2022 a Amurka.
Mai yiwuwa, nutsewar da wani kwale-kwalen ‘yan gudun hijirar Rohingya ya yi dauke da mutum 180, ya zamanto hadari mafi muni da ya auku a teku a ‘yan shekarun bayan nan.
Ana zargin Trump da tunzura magoya bayansa da suka kai hari a ginin Majalisar yayin da ake zaman tabbatar da nasarar da Joe Biden ya samu a zaben 2020. Sai dai Trump ya musanta zargin.
Wannan shi ne karo na uku da Argentina ke lashe kofin gasar, na farko a shekarar 1978 sai a 1986.
Najeriya na shirye-shiryen gudanar da babban zabe a watan Fabrairun badi, inda za a zabi shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin tarayya, sai kuma a watan Maris da za a yi zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha.
Hukumomin Amurkar sun ce za a gina tashoshin cajin ne a jihohi 35 da a sassan kasar a wani mataki na magance matsalar dumamar yanayi.
“Ka san makiyanmu suna bakin ciki ba mu samu matsala ba tsakaninmu da Mahamadou Issoufou, ji suke yi wai idan suka yi irin wadannan maganganu za su bata tsakaninmu.” In ji Bazoum.
Sakamakon wannan wasa na nufin Faransa za ta kara da Argentina wacce a ranar Talata ta doke Croatia da ci 3-0.
Wannan shi ne karon farko da wata kasa daga nahiyar Afirka da yankin kasashen larabawa, ta samu damar zuwa zagayen kusa da na karshe a gasar kofin duniya.
Taron na mayar da hankali ne kan yadda za a hada kai don bunkasa harkokin cinikayya da saka hannun jari da zai ciyar da tattalin arzikin Afirka gaba don a dama da nahiyar a fagen kasuwancin duniya.
A ranar Lahadi za a buga wasan karshe a gasar ta cin kofin duniya wacce Qatar ke karbar bakuncinta.
A watan Fabrairun bana, Rasha ta abkawa Ukraine da yaki, lamarin da kasashen duniya da dama suka yi Allah wadai da shi.
Wannan wasa dai ya dauki hankalin duniya duba da cewa kasashen biyu ba sa ga maciji a fagen siyasar duniya.
Sai dai yayin da wasu ke zumudin ganin ya sake tsayawa takarar, duba da irin sauye-sauyen da suke ikirarin ya samar, wasu kuwa cewa suke babu abin da ya tabuka a mulkinsa na farko.
Shi dai Biden wanda ya ka da Trump a zaben 2020, ya ce yana da burin ya sake tsayawa takara a zaben na 2024, amma kuma bai bayyana hakan a hukumance ba.
Gudau ya taka muhimmiyar rawa wajen garkuwa da dalibai da ‘yan kasashen waje a kananan hukumomin Kajuru, Chikun da Kachia a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A watan da ya gabata, Amurka, Birtaniya da wasu kasashen ketare suka fitar da sanarwa, inda suka yi kira ga ‘yan kasarsu da su yi hattara saboda akwai yiwuwar akai hare-haren ta’addanci a birnin na Abuja.
Hakan na faruwa ne yayin da jam’iyyar Republican ta gaza samun nasara a wasu yankuna, mai yiwuwa kuma jam’iyyar Democrat ta ci gaba da rike rinjayenta, duk da cewa bai taka kara ya karya ba.
PDP ta ce mutum 70 aka ji wa rauni, lamarin da ya kai ga kwantar da wasu asibiti.
Bayern ba ta yi karin haske kan girmar raunin na Mane ba, sai dai ta ce ba zai buga wasanta da Schalke a ranar Asabar ba.
Domin Kari