Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Zama Wajibi Mu Kalubalanci Sakamakon Zaben Shugaban Kasa – Atiku


Atiku Abubakar na PDP yana gabatar da taron manema labarai a Abuja, 02 Maris 2023
Atiku Abubakar na PDP yana gabatar da taron manema labarai a Abuja, 02 Maris 2023

Hukumar zabe ta INEC ta ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba zai iya gabatar da korafinsa a gaban kotu.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce wajibi ne su kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe ta INEC ta sanar.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai na kasa da kasa a ranar Alhamis a Abuja.

“Na tuntubi shugabannin jam’iyyata wadanda suna zaune a nan tare da ni, da sauran ‘yan Najeriya da ke sassa daban-daban, mun kuma yanke shawarar cewa yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa a ranar Asabar, akwai kura-kurai da dama, saboda haka, ya zama wajibi dukkan mu, mu kalulabalanci sakamakon.” Atiku ya ce.

Ya kara da cewa, masu aikin sa ido kan zaben na kasa da kasa da na cikin gida, duk sun bayyana yadda hukumar zaben ta INEC ta gaza wajen gudanar da aikinta.

Atiku ya kara da cewa, ya yi amannar cewa, wannan ba shi ne irin tarihin da Shugaba Muhammadu Buhari yake burin ganin ya bari ba, yana mai cewa, lokaci bai kure ba idan yana so ya saita al’amura.

Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar (tsakiya) tare da shugabannin jam'iyyar yayin da yake taron manema labarai a Abuja, 02 Maris, 2023
Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar (tsakiya) tare da shugabannin jam'iyyar yayin da yake taron manema labarai a Abuja, 02 Maris, 2023

Hukumar ta INEC ta ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba zai iya gabatar da korafinsa a gaban kotu.

A wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar a ranar Laraba, Shugaba Buhari ya ce zuwa kotu shi ne zabi mafi a’ala ga masu korafi ba zanga-zanga akan tituna ba.

A ranar Laraba, hukumar zaben Najeriya INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Tinubu ya samu kuri’a 8,794,726, abokin hamayyarsa na PDP, Atiku Abubakar ya samu kuri’a 6,984,520, sai Obi da ya zo na uku da kuri’a 6,101,533.

XS
SM
MD
LG