Babban bankin Najeriya CBN ya tsawaita wa’adin karbar tsofaffin takardun kudi zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu maimakon ranar 31 ga watan Janairu.
Darektan sashen kula da hada-hadar kudade a bankin na CBN, Ahmed Bello Umar ya tabbatar wa da Muryar Amurka ranar Lahadi.
Karin kwana goman na zuwa ne yayin da ya rage kwana biyu wa'adin da aka diba na daina karbar tsofaffin kudaden ya cika.
Jama'a da dama a Najeriya, ciki har da shugabannin siyasa da addinai sun yi ta magiyar neman a kara wa'adin, duba da cewa akasarin mutane ba su kammala mika tsoffin kudadensu ga bankuna ba.
A karshen makon da ya gabata, Gwamnan babban bankin na Najeriya Godwin Emefiele, ya fadawa manema labarai cewa ba-gudu-ba-ja-da-baya kan wa’adin na farko.
A cewar shi, kwana sama da 100 da aka ba ‘yan Najeriya su mika kudadensu ga bankuna, ya wadaci kowa ya kammala mika tsoffin kudaden.
“Kwana 90 ko 100 da muka bayar, ya ishi kowa ya mika tsoffin kudinsa a banki, kuma mun dauki matakan ba bankuna shawara su tsawaita ayyukansu don karbar tsoffin kudaden. Ni, a nawa tunanin, kwana 100 ya wadaci kowa.” Emefiele ya ce.
A ranar Juma’a bankunan Najeriya da dama suka sanar da cewa za su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi, a wani mataki na ba mutane Kofar shigar da tsoffin kudadensu.
Sai dai gwamnan bankin na CBN a ranar Lahadi, ya fitar da wata sanarwa wacce ta tsawaita wa’adin karbar tsoffin kudaden – bayan da ya nemi izini daga Shugaba Muhammadu Buhari.
“Lura da al’amuran da ke faruwa, mun nemi izinin shugaban kasa na kara kwana goma kan wa’adin, wato daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu, saboda mutane su samu damar mika tsoffin kudadensu na halaliya.” Sanarwar ta ce.