Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP da kotu ta sauke daga mukaminsa, ya ce zai daukaka kara kan hukuncin.
A ranar Juma’a kotun da ke sauraren kararrakin zabe a jihar Osun wacce ke kudancin Najeriya, ta soke nasarar da ya samu a zaben gwamnan da aka yi a watan Yulin bara.
Kotun ta ce an yi arangizon kuri’u a zaben, dalilin da ya sa aka soke kuri’un boge, lamarin da kuma ya rage kuri’un Adeleke yayin da na Adegboyega Oyetola suka karu.
“Ina so na yi amfani da wannan dama, na yi kira ga jama’armu, da su kwantar da hankalinsu. Za mu daukaka kara, kuma muna da yakinin cewa za a mana adalci.
“Kowa ya kwan da shirin cewa, za mu yi duk abin da ya kamata don ganin an dawo mana da nasararmu.” Wani sako da Adeleke ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a ya ce.
Rage kuri’un da aka yi aringizon su, ya sa kuri’un Oyetola suka karu zuwa 314, 921 yayin da na Adeleke suka ragu zuwa 290, 266.
Tuni dai kotun ta ba hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC umurnin ta karbe takardar nasarar da ta Adeleke ta ba Oyetola.