Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wa'adin Sauya Kudi: Za Mu Bi Umurnin Kotu, Amma Za Mu Kalubalanci Matakin – Malami


Ministan Shari'a Abubakar Malami (Facebook/Abubakar Malami)
Ministan Shari'a Abubakar Malami (Facebook/Abubakar Malami)

A ranar 15 ga watan Fabrairu kotun kolin za ta yi zama na gaba don ci gaba da sauraren karar.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta bi umurnin da kotun kolin kasar ta bayar na dakatar da aiwatar da wa’adin daina amfani da tsofaffin kudade a kasar.

A ranar Laraba kotun kolin ta ba da umurni ga bankunan kasar da su jingine wa’adin har sai yadda karar da aka shigar ta kaya.

A farkon makon nan jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara suka maka gwamnatin Najeriya a kotu kan shirin aiwatar da wa’adin hana amfani da tsoffin takardun kudaden 200, 500 da 1000.

Yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na Arise TV a ranar Alhamis, Ministan Shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya ce za su bi umurnin, amma za su kalubalance shi a zama na gaba.

Da farko babban bankin Najeriya na CBN ya saka wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudaden akan ranar 31 ga watan Janairu.

Amma an tsawaita wa’adin zuwa 10 ga watan Fabrairu bayan korafe-korafe da jama’a ke ta yi.

Al’umar Najeriya na fuskantar karancin sabbin takardun kudaden 200, 500 da 1000 da aka sauyawa fasali, lamarin da ya haifar da dogayen layuka a bankunan kasar.

Rahotanni sun yi nuni da cewa an kai hare-hare kan wasu bankuna a wasu sassan kasar.

Bankin na CBN ya dora alhakin hakan akan masu boye kudaden don biyan bukatun kansu.

A ranar 15 ga watan Fabrairu kotun kolin za ta yi zama na gaba don ci gaba da sauraren karar.

XS
SM
MD
LG