Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Kafa Kwamitin Da Zai Mika Mulki Ga Sabuwar Gwamnati


Lokacin da Buhari yake jawabi a ziyarar da sanatoci 22 da ke barazanr komawa PDP suka kai masa a bara(Hoto: Facebook/Fadar shugaban kasa)
Lokacin da Buhari yake jawabi a ziyarar da sanatoci 22 da ke barazanr komawa PDP suka kai masa a bara(Hoto: Facebook/Fadar shugaban kasa)

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, wanda shi zai jagoranci kwamitin ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja.

Rahotanni daga Najeriya na cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kafa kwamitin da zai mika mulki ga sabuwar gwamnatin da za a zaba.

A ranar 25 ga watan Fabrairu Najeriya za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Za kuma a mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun bana.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, wanda zai jagoranci ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja.

Rahotannin sun yi nuni da cewa, Mustapha shi zai jagoranci kwamitin na mika mulki.

Cikin kwamitin har ila yau akwai shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, babban hafsan sojin Najeriya, Sufeta Janar na ‘yan sanda da sauransu.

A ranar 14 ga watan Fabrairu za a kaddamar da kwamitin, wanda zai jagoranci ragamar shirye-shiryen mika mulki ga sabuwar gwamnatin da za ta shigo.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG