Tun bayan da babban bankin na Najeriya ya kara wa’adin daina amfani da tsoffin kudaden naira daga 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu, sabbin kudaden nairar na ci gaba zama kamar almara, domin duk bankin da ka leka sashen injin din cire kudi na ATM sai ka ga dogon layi.
Wasu rahotanni sun ce akwai mutanen da kan kwana a kofar banki yayin da wasu ke tafka sammakon don kama layi.
A karshen makon da ya gabata ne, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya rarrashi ‘yan Najeriya inda ya nemi da su ba shi kwanaki bakwai domin kawo karshen wannan matsala, yayin da shi kuma babban bankin kasar na CBN, ya umarci bankuna da su fara ba da sabbin kudaden a cikin bankin ba a injinan ATM kadai ba.
Yayin da ake kokarin kashe wutar wannan matsala ta karancin sabbin kudaden naira, wutar wata matsala ce ta daban, ita ma take ci gaba da ruruwa a sassan kasar – wato matsalar karancin man fetur, yanzu haka akwai dogayen layin motoci da ke kokarin sayen fetur a gidajen Man babban birnin Abuja.
Hukumomin Najeriya dai sun ce suna kokarin shawo kan wannan matsala ta karancin man fetur, yayin da ya rage ‘yan makonni a gudanar da zaben shugaban kasa.
Domin karin bayani ga cikakken rahotan Mahmud Lalo: