Manyan jami’an sun yi wadannan kalaman ne yayin wani taro da ya hada har da shugaban hukumar zabe ta INEC, wanda ya gudana a ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro a Abuja.
Taron wanda ya samu halartar babban hafsan sojin Najeriya Janar Lucky Irabor, da manyan hafshin sojin kasar da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, ya tabo batutuwa da dama, wadanda duk sun ta’allaka ne kan zaben da ke tafe.
Manyan jami’an tsaron na Najeriya sun yi jawabi daya-bayan-daya inda suka kore duk wani fargaba da al’umar kasar ke nunawa dangane da zaben, wanda suka ce za a yi lami lafiya.
Manjo Janar Babagana Monguno da ya karbi bakuncin taron, shi ne ya fara jawabi
Ya ce "muna sane da halin da kasar nan take ciki, akwai bukatar in karawa al’umar Najeriya kwarin gwiwar cewa, idan suna da wani fargaba a zuciyarsu, ina so na kore musu wannan tunani, zaben 2023 zai gudana cikin Lumana.”
A cewar Monguno, akwai mutanen da suke yada karerayi a kafafen sada zumunta da nufin ta da husuma ko tsorata mutane, yana mai cewa, hukumomin tsaron kasar sun dauki kwararan matakan da za su tabbatar an gudanar da zaben lami-lafiya.
“Duk wani da yake da burin ya ga ya kada kuri’arsa kamar yadda doka ta ba shi dama, zai kada kuri’arsa cikin yanayi na cikakken tsaro.”
La’akkari da cewa jami’an ‘yan sanda su ke da alhakin tabbatar da tsaro a lokacin zaben, shugaban ‘yan sandan Najeriya, Sufeta Janar Alkali Baba ana shi bangare ya ce a shirye suke tsaf.
“Ina so in ba ku tabbacin cewa, ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun shirya domin ganin zaben ya gudana ba tare da wata matsala ba.”
Yayin jawabinsa, shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce suna da kwarin gwiwa matakan da jami’an tsaro suka dauka za su yi tasiri, yana mi nuni da karin tsaro da aka saka a ofisoshinsu da ke sassan kasar.
Gabanin zuwansa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Farfesa Yakubu ya yada zango a babban bankin kasar na CBN inda ya mika bukatar ganin an samawa hukumar kudade don ta gudanar da ayyukan aika kayayyakin zabe zuwa jihohi, yayin da ake fama da karancin sabbin takardun kudade da aka sauyawa fasali.
Gwamnan babban bankin na Najeriya, Godwin Emefiela, ya ce bankin nasa a shirye yake wajen ganin ya biya wa hukumar ta INEC bukatarta.
“Babban bankin na Najeriya ba zai bari a yi amfani da shi ba, ko kuma a yi masa kallon ya kawo cikas a kokarin da ake yi na ganin an tabbatar da sahihin zabe ba.”
A ranar 25 ga watan nan na Fabrairu, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki sai kuma a ranar 11 ga watan Maris a gudanar da gwamnoni da na ‘yan Majalisun jiha.
Zaben na ci gaba da karatowa ne, yayin da Najeriyar take fuskantar matsalar karancin sabbin kudaden da aka sauya fasali da ta karancin man fetur baya ga matsalar tsaro da ta jima tana addabar wasu sassan kasar.
Saurari rahoton a sauti: