Sai dai hukumar zabe ta INEC, ta ce ta gudanar da ayyukan yin rijista a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke fadin Kananan hukumomin jihar Sokoto, domin su ma a ba su dama su yi zabukan da ke tafe.
Jihar Sokoto, ta kasance daya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga suka addaba a arewa maso yammacin Najeriya a ‘yan shekarun baya-bayan nan, lamarin da ya haifar da kwararar dubban ‘yan gudun hijira da ke neman mafaka a sansanoni daban-daban a jihar, wadanda aksarinsu ba a gidajensu na asali zaben da ke tafe zai riske su ba.
Sai dai yayin da wasu ke cewa sun samu katin zabensu, a gefe guda, wasu cewa suka yi ba su samu na su katin ba.
Malama Rabi Isa ‘yar hijira ce da ke zaune a sansanin ‘yan gudun Hijra na Ramin Kura a Sakkwato. Ta ce ta kuduri aniyar yin zabe a wannan shekarar, saboda muhimmancinsa amma har ya zuwa yanzu bata da katin zabe.
Ita kuwa Malama Luba, wacce makonta guda a wannan sansanin ‘yan gudun hijira na Ramin Kura dake jihar Sokoto, ta ce har yanzu ba ta da katin zabe, amma wadanda suka samu, tuni sun riga sun san rumfanan zaben da za su kada kuri’unsu.
Bashiru Altine Guyawa, dan fafatukar kare hakkin bil Adama ne, ya kuma ce akwai bukatar hukumar ta INEC ta saurari koken ‘yan gudun hijirar
To sai dai hukumar ta INEC ta ce ta riga ta gudanar da ayyukan rijistar a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar ta Sakkwato tare da sama musu rumfunan da za su yi kada kuri’unsu. Kamar yadda jami’i a hukumar ta INEC da ke wayar da kan jama’a kan al’amuran zabe ya bayyanawa sashen Hausa na Muryar Amurka.
A ranar 25 ga watan nan na Fabrairu, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya sai kuma a ranar 11 ga watan Maris a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.
Domin Karin bayani saurari rahotan Mahmud Lalo: