Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Hare-hare A Najeriya


Tsohon Hoto: Wani hari da 'yan bindiga suka kai a arewacin Najeriya a shekarun baya
Tsohon Hoto: Wani hari da 'yan bindiga suka kai a arewacin Najeriya a shekarun baya

Yayin da wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ke shirin karewa , jama’a da dama za su zura wa magajinsa ido don ganin yadda zai shawo kan matsalar ta hare-hare a Najeriya.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun yi kira ga hukumomin Najeriya da su kawo karshen hare-haren da ke salwantar da rayukan al’uma a kasar.

Kiran na zuwa ne bayan wasu hare-hare da suka yi sanadin mutuwar mutum 35 a jihohin Katsina da Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya a karshen makon da ya gabata.

Kungiyar Amnesty International na daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil Adama da suka yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a kwanan nan a arewacin kasar.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, kungiyar ta nemi hukumomin Najeriya da su dauki matakan gaggawa wajen kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a kudancin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

A ranar Asabar ‘yan bindiga dauke da manyan makamai suka far wa kauyen Unguwar Wakili da ke yankin Zangon Kataf suka kashe mutum 15, mafi aksarinsu mata da da kananan yara.

Cikin shekaru da dama, wannan yanki ya sha fuskantar rikicin manoma da makiyaya, lamarin da ke haddasa asarar dubban rayuka.

Kungiyar ta Amnesty ta ce an kashe akalla mutum 366 tsakanin watan Janairu da Yulin shekarar 2020.

“Hukumomi suna nuna gazawa wajen hukunta wadanda suke kitsa wadannan hare-hare – abin takaici ne, idan aka yi la’akkari da cewa an jima ana kai ire-ire wadannan hare-hare, sam ba zu mu lamunci hakan ba.” In ji Aminu Hayatu, kakakin kungiyar ta Amnesty International.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna ta ce tana kan gudanar da bincike, amma sakamakon binciken farko ya nuna mata cewa harin na daukar fansa ne bayan da aka kashe wani makiyayi yayin da yake kiwo a kwanakin baya.

Kakakin ‘yan sanda Muhammad Jalige bai amsa waya ba a lokacin da muka tuntube shi kan wannan lamari.

“Kullum matsayar gwamnati ita ce, ana kan gudanar da bincike, amma babu wata rana guda da aka fada mana sakamakon binciken da suke ikirarin suna yi, hakan kuma abin damuwa ne, domin yana karawa masu kitsa wadannan hare-hare kwarin gwiwa.” Hayatu ya kara da cewa.

Najeriya na fama da matsalolin tsaro ta fuskoki da dama, wadanda suka hada da hare-haren ta’addanci, garkuwa da mutane don neman kudin fansa, da kuma fadan kabilanci.

A wani hari na daban da aka kai a karshen makon da ya gaba, ‘yan bindiga sun kashe akalla mutum 20 a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya a cewar ‘yan sanda.

Isa Gambo, shi ne Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar ta Katsina, ya kuma ce tuni hukumomi suka maido da zaman lafiya a yankin da lamarin ya faru.

“Maharan daga Zamfara suka fito akan Babura, suka shiga cikin Katsina. Ko da yake, al’umar yankin, ‘yan sanda da sojoji da sauran jami’an tsaro sun yi kokari wajen dakile harin, har jirgin sama muka tura, sai dai mutum 20 sun mutu wasu kuma da dama sun jikkata.”

A watan da ya gabata ne miliyoyin ‘yan Najeriya suka gudanar da zaben shugaban kasa.

Yayin da wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ke shirin karewa , jama’a da dama za su zura wa magajinsa ido don ganin yadda zai shawo kan matsalar ta hare-hare a Najeriya.

Saurari fassara rahoton Timothy Obiezu:

Kungiyar Amnesty Ta Yi Allah Wadai Da Hare-haren Najeriya.mp3 - 3'07
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

XS
SM
MD
LG