Hare haren da aka ta samu cikin kwanakin nan, ya nuna cewa mayakan Boko Haram sun sauya salon hare-haren da suke kaiwa inda suka koma amfani da kananan yara wajen tada bama-bamai.
A daren jiya Alhamis ne aka samu tashin wani bam da ya kashe wasu kananan yara biyu ya kuma jikkata wasu a unguwar Fadaman Rake dake garin Hong a jihar Adamawa.
Bayan da Atiku Abubakar, ya zama Wazirin Adamawa dansa Aliyu Atiku Abubakar ya zama sabon Turakin Adamawa
Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani sabon rikici ya sake kunno kai a jam’iyar APC game da batun sake tsayawa takarar gwamnan jihar Sen. Muhammadu Bindo Jibrilla a shekarar 2019.
Ma’aikata a jihar Adamawa na kokawa sakamakon zaftare musu albashi domin yin katin shaidar ma’aikata wato ID Card, batun da ma’aikatan suka ce ba zata sabu ba.
Yayin da kwamitin duba batun Karin albashi ke cigaba da aikin tabbatar da batun, yanzu haka masana na ganin akwai abun dubawa.
Yiwa Najeriya da shugabaninta addua ya zama wajibi ga 'yan Najeriya domin samun zaman lafiya da karuwar arziki
Gwamnatin Najeriya ta nuna alamun kyautatuwar alkaluman tattalin arziki a daidai lokacin da talakawa ke kokawa kan tsadar rayuwa. Sai dai kuma wasu daga cikin ‘yan kasauwar sunce su basu fara gani a kasa ba.
Yanzu haka an sake tura ‘karin jami’an tsaro zuwa yankin Takum da Ussa na jihar Taraba, biyo bayan kazancewar rikicin Fulani makiyaya da kuma yan kabilar Kuteb manoma.
Gwamnatin jihar Adamawan dake cikin jihohi uku da rikicin Boko Haram yafi shafa, ta musanta zargin cewa ta soma korar yan gudun hijiran dake jihar.
Tuni wasu suka fara kada gangar tazarce a Najeriya ganin cewa sun gamsu da yadda mulkin kasar ke gudana
Yanzu haka kungiyoyi da kuma kuma dattawan jihar Taraba na maida martani game da kalaman da gwamnan jihar Taraba Arch. Darius Dickson Isiyaku, na danganta rikicin da aka samu a tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu kabilu a jihar da Boko Haram, batun da suka ce bai dace ba.
Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa yanzu hankulan iyaye na tashe sakamakon yawaitar fyaden da ake yiwa kananan yara.
Yanzu haka an fara cece-kuce a jihar Adamawa game da batun sauya sheka da ake cewa wasu kusoshin jam’iyar PDP a jihar sun yi zuwa jam’iyar APC, batun da su ‘yan PDP ke cewa cewa wannan batu ba gaskiya bane.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Taraba ta kama wani mutum daya kashe wani yaro karami ya kuma sara shi gunduwa –gunduwa.
Bayan doguwar cece-kuce yanzu haka an kawo karshen takaddamar sabon sarkin Jada, dake kudancin jihar Adamawa, inda yanzu aka samu sabon sarki Alhaji Umar Ardo.
Gwamnatin jihar Adamawa ta gudanar da bikin baiwa mai martaba sabon sarkin Shelleng Dr Abdullahi Isa Dasong sandar girma mai daraja ta daya, inda jama’a daga sassa daban-daban na ciki da wajen jihar suka halarta.
Bikin kamun Kifin Geriyo na bana ya yi Albarkar Kifi sai dai babu kudade a hannun jama'a
Yayin da a Najeriya hukumomi ke tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, hadakar kungiyoyin nakasassu a kasar na kukan cewa ba’a tunawa dasu.
Hukumar kare hakkin dan Adam a Najeriya da kungiyar direbobi ta NURTW sun yi kira ga shugabanin hukumomin tsaro a kasar da su gudanar da bincike game da matakin da gwamnatin jihar Taraba ke dauka a yanzu na iza keyar baki yanci rani da kuma karbe musu kudaden da ake zargin ana yi.
Domin Kari