Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manazarta Kan Karin Albashi A Najeriya Sun Ce Akwai Abin Dubawa


Yayin da kwamitin duba batun Karin albashi ke cigaba da aikin tabbatar da batun, yanzu haka masana na ganin akwai abun dubawa.

Tun a cikin watan Mayun bara ne dai ma'aikatan kasar suka mika wata bukatar karin albashin da ya kai na kusan Naira 56,000 ga gwamnatin da nufin rage radadin janye tallafin man fetur a kasar. Kuma an dauki lokaci ana tattaunawa a tsakanin ma'aikata da gwamnatin kafin mika wani rahoto ga gwamnatin kasar a cikin watan Afrilun da ya shude.

An sha tafka dogon turanci da muhawara a tsakanin gwamnatin da ke korafin rashin kudi da wasu jihohi da ke tafiyar hawainiya dakuma wadanda suka kasa biyan albashin ma'aikatan da ke fadi tashin tsadar rayuwa. Kuma wannan tattaunawar na zuwa ne a dai dai lokacin da tattalin arzikin tarrayar Najeriyar ke nuna alamun harbawa.

To sai dai kuma yayin da ake wannan batu manazarta na ganin akwai abun dubawa game da batun Karin albashin. Hon.Abdullahi Prembe, dan siyasa kuma masanin tattalin arziki ya ce ba karin albashi ne matsala ba, kamata yayi a dau wasu matakan kandagarki.

Shi ko Yusha'u Aliyu wani masanin, na ganin karin albashi ba shi ke kawo hauhawar farashin kayayyaki ba.

To ko ya suka ji da wannan batu? Komred Dauda Maina, shine shugaban kungiyar kwadago a jihar Adamawa, ya bayyana fatan da suke yi a yanzu.

Ga rahoton Ibrahim Abdul’Aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG