Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Abubakar Ya Ce Bindo Jibrilla Tazarce Kawai


 Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani sabon rikici ya sake kunno kai a jam’iyar APC game da batun sake tsayawa takarar gwamnan jihar Sen. Muhammadu Bindo Jibrilla a shekarar 2019.

Yanzu dai abun boye ya bayyana fili game da rikicin da ke akwai a jam’iyar APC a jihar Adamawa, biyo bayan ce ce ku ce dake gudana tsakanin bangarori biyu na jam’iyar a jihar.
Da farko dai gwamnan jihar Sen.Muhammadu Bindo Jibrilla ya zawarto wasu tsoffin kusoshin jam’iyar PDP da a baya suka goyon bayan tsige gwamnatin Murtala Nyako, ciki ma harda tsohon babban hafsan sojin Najeriya Alex Badeh da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar domin su mara masa baya inda kuma ba tare da bata lokaci ba,Atiku, Alex Badeh, Jibril Aminu dama sauran wadanda suka gabatar da jawabai a taron masu ruwa da tsaki ke cewa Bindow Tazarce!
Da yake jawabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar cewa yayi sukan Bindo Tazarce,yana mai cewa ‘’ Ai kowa ya ga irin ayyukan da aka yi wanda tun da aka kafa Adamawa ba’a samu gwamnan da yayi aiki kamar Bindow ba, don haka muna tare da shi,ya cigaba,’’ a cewar Atiku.
To sai dai kuma suma yan APC Amana dake tare da bangaren su Murtala Nyako, Mijinyawa Kugama, Nuhu Ribadu, Babachur David Lawal, Janar Buba Marwa, Engr Gudiri sun gudanar da nasu taron inda suka caccaki daya bangaren da cewa tsintattiyar mage wai bata mage.
Alh.Uba Dan Arewa dake wannan bangaren ya bayyana yadda tafiyar take a yanzu.
Ya zuwa yanzu an zura ido aga yadda wannan dambarwa zata kaya,yayin da masana siyasa irinsu Hon.Abdullahi Prembe ke ganin za’a debi yan kallo a shekarar 2019,kasancewar guguwar sak ka iya sauyawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG