Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Abubakar Ya Zama Wazirin Adamawa


Atiku Abubakar Wazirin Adamawa
Atiku Abubakar Wazirin Adamawa

Bayan da Atiku Abubakar, ya zama Wazirin Adamawa dansa Aliyu Atiku Abubakar ya zama sabon Turakin Adamawa

Yanzu dai batun ko wa zai zama sabon wazirin Adamawa ya zo karshe biyo bayan nada tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin sabon Waziri kana dansa kuma Aliyu aka bashi mukamin mahaifinsa na Turakin Adamawa.

A watan jiya ne Allah ya yiwa tsohon Wazirin Adamawan Alhaji Abba Mohammad rasuwa bayan rashin lafiyar da yayi fama da ita.

Tuni dai ‘yan majalisar masarautar Adamawa suka kai caffar mubaya’a ga sabon waziri Atiku Abubakar da kuma dansa wato sabon Turakin Adamawa Aliyu Atiku Abubakar, wanda da yake jika ga marigayi lamido Aliyu Mustapha.

Galadiman Adamawa Mustafa Aminu shi ya jagoranci hakimai da sauran kusoshin fada zuwa wannan mubaya’ar.

Da yake maida jawabi, Atiku Abubakar ya saba layar cewa zai hada kan sarakunan masarautar domin kawo hadin kai da fahimtar juna.

Kamar yadda yake a bisa al’ada,Waziri shine na biyu bayan sarki, wanda hakan yasa kawo yanzu jama’a suka soma bayyana ra’ayoyinsu game da wannan sarautar Waziri tare da aza tambayar ko shin Atiku zai ajiye siyasa ya koma fada, ko kuma a’a. Kuma koma menene dai lokaci ne kawai zai iya bada amsar wannan tambayar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG