Rikicin Boko Haram dai ya lakume rayuka da dama, baya ga wasu dubban da aka tilastawa gudun hijira, kuma wani fannin da ba’a cika maida hankali ba shine halin da nakasassu suka shiga.
A wajen wani taron masu ruwa da tsaki na sabuwar kungiyar nakasassun Najeriya ta Progressive Disabled Forum, PDF, Kwamrad Ibrahim Alhassan Ganye, dake zama shugaban kungiyar a Najeriya, ya ce rikicin Boko haram ya maida wasu nakassasu, kuma abin takaici kawo yanzu hukumomi da kuma kungiyoyin agaji basa tunawa dasu a tallafin da ake badawa domin tada komadar al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa.
Hakan yasa shugaban kungiyar ya mika kukansu ga gwamnatocin arewa da kuma kungiyoyin bada agaji da ake tunawa dasu.
Ita kuwa Patience Briston, dake cikin wadanda rikicin Boko Haram ya nakasa biyo bayan tashin wani bom da ya rutsa da ita a garin Maiduguri, tace an maida su saniyar ware.
Kafin dai wannan rikici na Boko Haram gwamnatocin jihohin kan taimaka wajen kafa cibiyoyin koyon sana’a ga nakasassu shirin da a baya kwalliya ke biyan kudin sabulu.
Koda yake kullum dai gwamnatocin jihohi kan ce suna nasu kokari, to amma kuma sukan danganta rashin kudi da zama kanda –garkin halin da nakasassun ke ciki, kamar yadda gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ke cewa.
Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum