Tun farko ma dai saida wasu kungiyoyi a yankin 24 rubuta takardar korafi wanda suka aikewa mai martaba gwangwari Ganye da kakakin Majalisar Dokokin jihar da kuma mai martaba Lamidon Adamawa, dake zama shugaban Majalisar Sarakunan jihar game da batun nadin Umar Ardo a matsayin sabon sarki.
Kafin nadin sarkin Jada, an kai ruwa rana a yankin a tsakanin bangarorin dake neman kujerar, sai dai kuma yanzu za’a iya cewa an sasanta lamarin da yakai ga shirya bikin nadin sabon sarkin Jadan Alhaji Umar Ardo.
Jada da dai yanki ne dake da manyan yan siyasa da kuma ‘yan boko da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. To sai dai kuma batun gadar tsohon sarkin da ya rasu, ya so ya raba kawunan shugabanin yankin inda wasu ke goyon bayan dan sarki mai rasuwa yayin da wasu kuma ke marawa Sabon sarki Alhaji Umaru Ardo.
Da yake jawabi wajen nadin sabon sarkin, mai martaba gwangwari Ganye dake zama shugaban majalisar masarautar Ganye da ta kunshi kananan hukumomin Ganye da Jada da kuma Toungo, Alhaji Umaru Adamu Sanda, ya bukaci al’ummar Jada ne dasu baiwa sabon sarkin da aka nada hadin kai domin ciyar da yankin gaba.
Shima a jawabinsa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya godewa al’ummar masarautar ne game da fahimtar juna da kuma hadin kai da aka soma samu.
Shi dai sabon sarkin Umar Ardo, nuna farin cikinsa yayi da kuma yabawa gwamnatin jihar bisa ayyukan da aka fara a yankin.
Duk dai da hatsaniyar da aka samu a tsakanin wasu matasan siyasa an kamala bikin nadin sabon sarkin lafiya, inda aka gudanar da raye-rayen gargajiya na kabilun yankin.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum