Kafin ma dai wannan sabon mukamin Dr Abdullahi Isa Dasong na biyu, shine hakimin cikin garin Shelleng, da kuma sabon nadin nasa ya zama sarki na 21 a cikin jerin sarakuna Shelleng.
Baya dai ga yan kabilar Kanakuru, wanda su ke Sarauta, haka nan akwai wasu kabilu da dama a yankin da suka hada da Lala da Fulani kitaku da libo, kana kuma da sauran kabilun da aiki ko kasuwanci ya kawo su to amma yanzu suka zama yan kasa.
Da yake jawabi a bikin bada sandar girman, gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, ya ce gwamnatinsa zata cika alkawarin data yiwa al’ummar yankin Shelleng na kamala aikin hanyar garin da suka dade suna fatan ganin an kamala.
Yanzu haka dai sabon sarkin da aka nada, na fa cikin farin ciki tare da mika godiyarsa dangane da hayewa kujerar da yayi, yayin da suma al’ummar masarautar ke fatan alheri.
Shima mai martaba sarkin Shani, dake jihar Borno, Alhaji Muhammmad Nasir mai lafiya na biyu, na daga cikin manyan sarakunan da suka hallarci bikin ya kuma bayyana alakar dake akwai a tsakanin Shani da Shelleng.
Idan za’a iya tunawa makwanni da rasuwar tsohon sarkin Shelleng, a jihar Adamawan, wato marigayi Abdullahi Managina sarki mai daraja na daya, biyo bayan doguwar rashin lafiyar da yayi fama da ita, shine aka nada sabon sarki don maye gurbin sarkin da ya rasu, wanda ya fito daga gidan sarautar Isa Dasong.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’Aziz.
Facebook Forum