Dattawan jihar na maida martani ne game da kalaman da gwamnan jihar Taraban yayi lokacin da yake tarban hafsan soji mai kula da runduna ta 82, dake Enugu wato GOC Manjo Janar Adamu Abubakar, wanda ya kai ziyarar aiki jihar, inda gwamnan Taraban ya danganta tashe tashen hankulan da ya faru tsakanin Fulani makiyaya da wasu kabilun jihar da cewa ‘yan Boko Haram suka tsallako jihar.
A wajen wani taron manema labarai a Jalingo fadar jihar, Alhaji Hassan Jika Ardo, tsohon shugaban jam’iyar APC a Taraba, ya musanta kalaman gwamnan da cewa hakan bai dace ba.
Hassan Jika Ardo, wanda ke cikin wadanda aka tantace a matsayin Jakada wato Ambassada, yace a matsayinsu na shugabanin al’umma basu ji dadi da kalaman dake fito daga bakin gwamnan ba, da yace hakan na iya maida hannun agogo baya a yunkurin da ake yin a gano bakin zaren magance rikicin kabilanci da ake samu a jihar.
To sai dai kuma gwamnan ta bakin hadiminsa ta fuskacin harkokin yada labarai Mr Sylvanus Giwa, ya ce ba haka kawai yayi wadannan bayanai ba.
Tun farko ma dai a jawabinsa, hafsan sojin mai kula da runduna ta 82 dake Enugu wato GOC Manjo Janar Adamu Abubakar, yace yaje jihar Taraba ne don gano bakin zaren magance rikicin Fulani makiyaya da manoma dama sauran batutuwan da suka shafi tsaro, inda ya bada shawarar kafa kwamitin tsaro a jihar da zai kunshi shugabanin al’umma, yayin da a nata bangaren rundunan yan sandan jihar ta gargadi al’ummar jihar da a dai na tunzura jama’a ko kalaman da ka iya kawo tashin hankali.
Jihar Taraba dai jiha ce dake da yawan kabilu wanda kuma ta sha fama da tashe tashen hankula dake da nasaba da fadan kabilanci wanda sau tari kan rikide ya koma na addini.
Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum