Da yake nuna takaicinsa bisa tashin bam da ya afku da wasu kananan yara a Fadamar Rake,cikin karamar Hukumar Hong,gwamnan jihar Adamawa Sen.Muhammadu Bindow Jibrilla ya gargadi jama’a ne da suke sa ido.
Gwamnan wanda yace gwamnatin jihar ta dauki nauyin wadanda suka jikkata tare da jajantawa iyayen yaran da suka rasu,yace wannan wani sabon salo ne da yan ta’adda suka bullo da shi don cutar da jama’a.
Ita ma dai hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya NEMA, wanda ta nuna kaduwarta da wannan lamari,tace yanzu haka bayanai na nuni da cewa mayakan Boko Haram sun sauya salon hare-haren da suke kaiwa,wanda domin haka hukumar tace a kulla. Sa’adu Bello babban jami’in hukumar ta NEMA,mai kula da jihohin Adamawa da Taraba,ya bayyana wuraren da ya kamata a sa ido.
A makwannin baya jama’a sun tashi tsaye wajen tsaron massalatai majami’u, kasuwanni da ma wuraren hada hadar jama’a.To sai dai yanzu da alamun an soma sakaci.
Kawo yanzu,rikicin Boko Haram da aka shafe fiye da shekaru bakwai ana fama da shi,ya fa lakume dubban rayuka baya ga wadanda aka tilasatawa yin gudun hijira,koda yake yanzu lamurra sun fara komawa daidai a wasu wuraren.
Facebook Forum