A soma shirye-shiryen bukukuwan cika shekaru biyu na gwamnatin APC a Najeriya, kowa ce shekara gwamnatoci a daidai wannan lokaci kan shirya bukukuwan ranar demokaradiyya inda akan yi bita nasarorin da aka samu.
To sai dai kuma yayin da ake shirye shiryen cika shekaru biyu yanzu haka kawunan sun rabu musamman game da batun rashin lafiyar shugaban kasar da tuni wasu suka fara kiraye-kirayen cewa ya kyautu shugaba Buhari yayi murabus, yayin da wasu kuma ke ganin ko a shekarar 2019, Buhari zasu zaba.
Hon. Rufai Umar Gombi dan majalisar dokokin jihar Adamawa ne dake tallata tazarcen Buhari-Osibanjo wato Buhari/Osibanjo Again,yace sufa suna nan daram.
To sai dai kuma wasu na ganin ana siyasantar da batun rashin lafiyar shugaban kasa ganin yadda ya koma jinya, kana kuma ga batun da wasu ‘yan Najeriya ke yi a yanzu haka cewa yayi ko kada yayi murabus.
Muhammad Ibrahim editan jaridar Ahlul-Bayt a Najeriya yace akwai wani abu akan matar sarki, wai da da ido da ta gani.
Batun cin hanci da rashawa yana cikin abubuwan da gwamnatin APC ta kudiri aniyar kawarwa, inda kawo yanzu aka bankado badakala da dama, koda yake wasu na ganin akwai abun dubawa.
Hon. Abdullahi Prembe tsohon kwamishinan yada labarai a jihar Adamawa, ne ya bayyana yadda suke kallon tafiyar a yanzu.
Ko ma da menene dai yanzu lokaci ne kawai ka iya tabbatar da yadda zata kaya kafin nan da shekara ta 2019.
Facebook Forum