Hukumomin Jihar Tahoua a Jamhuriyar Nijar, sun gana da sarakunan gargajiya, da kungiyoyin manoma da na makiyaya, domin tunkarar lokacin bayan damuna, inda ake fuskantar fada a wadansu yankunan kasar tsakanin manoma da makiyayan da ke iya kai ga asarar rayuka da dama.