Zamu soma labarun wassaninmu na yau da gasar kwallon kafa mafi farin jini a duniya ta kulob – kulob ta zama zakara a kasashen nahiyar Turai, inda yanzu haka, ana can ana kabsawa tsakanin Bayern Munich da PSG a Parc Des Princes na Birnin Paris a kasar Faransa, inda yanzu Bayern ke gaba da 1-0.
Wasan tsakanin wadannan kungiyoyin shi ne mafi zafi a wannan matakin na 16 na kombalar ta Champions League ta wannan shekara ta 2023.
Wasan na 2 dake wakana a yau na hada Milan AC ta kasar Italiya da Tottenham ta kasar Burtaniya.
Game da wadannan wassanin 2 na yau Talata na Champions League na Turai, na hiranta da daya daga cikin ma’abutan sh’anin kwallon kafa a nan Birni N’Kooni, kamar yadda za a ji ta sauti.
Za a ci gaba da wadanan wasannin a ranar gobe Laraba inda kungiyar Club de Bruges na Beljium ke karawa da Benfica ta kasar Portugal sai Dormund ta kasar Jamus zata goga da Chalsea ta kasar Ingila
Shi ko Danis Alves, dan wasan kwallon kafa na Brazil na ci gaba da fuskantar tuhuma daga kotun kasar Spain biyo bayan zargin yi wa wata matashiya Fade.
Daga cikin matakan da kotun kasar ta Spain ta dauka a kan dan wasan, har da karbe passport din sa na Spain da na Brazil da ma saka masa wata munduwa mai aiki da na’ura domin sanin inda yake a kowane lokaci.
Sai dai dan kwallon mai shekaru 37 a duniya, da a ka zarga tun 30 ga watan Disamban da ya gabata, da yin fade wa matashiya yar shekaru 23 da haihuwa, ya canza maganar sa sau 3, abin da ke iya sawa ya kara samun matsala a wannan shari’a.
Saurari cikakken rahoton Haruna Mammnan Bako: