Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taro Kan Matsalar Tabarbarewar Tarbiyya, Ta'addanci A Nijar


Kungiyar matasa ta Nijar da AJIKAD Nijar, da kuma kungiyar matasan Nijar Musulmi, sun shirya wani taro tare da jami'an tsaron kasar domin neman hanyoyin samarwa matasan dauki game da maganar ta'adanci da tabarbarewar tarbiya.

BIRNIN N’KONNI, NIGER - Kungiyar AJIKAD Nijar ce, tare da kungiyar matasa Musulmi ta Jamhuriyar Nijar (club des jeunes musulmans du Nijer) a Faransance, suka shirya taron a garin Tahoua domin fadakar da matasan ta la'akari da tabarbarewar tarbiya da suka hada da rashin aiki da shaye-shaye da ke ingiza matasan shiga ta'adanci.

Kungiyoyin da suka hada da jami'an tsaro a wurin taron suna yunkurin kawowa matasan dauki ne, domin ceto su daga fadawa a cikin miyagun halaye da ke ingiza su a tarkon ‘yan ta'adda, kamar yadda Suleymane Alhadji Buzu Malick daya daga cikin shugabanin da suka shirya wannan taron ya gaya mana.

Sai dai ana rara sai ga dare yayi inji hausawa, wannan fadakarwa da wadanan kungiyoyin kewa matasan maza da mata na zuwa ne, a daidai lokacin maganar dokar auren jinsi guda ke ci gaba da daukar hankullan ‘yan kasar, sane da cewa, matasa ne ke aikata irin wannan dabi'ar da asalin ta gurbacewar tarbiya ce injin wadansu matasa mahalarta taron.

Maganar ta'adanci ita ce tafi daukar lokacin mahalarta taron kasancewa, ‘yan ta'adar da jami'an taron da ke fatatakarsu dukkan su matasa ne a bayanin da Suleymane Alhadji Buzu Malick ya yi mana.

A wurin wannan ganawar an canza miyaw sosai tsakanin matasan da jami'an tsaron, inda bangarorin biyu suka amince cewa sai sun hada karfi da karfe idan suna son shekarsu ta cimma ruwa inji Babban Komishinan ‘yan sanda na Jihar Tahoua Malam Muntari Abdu.

Daga karshe bangarorin da suka halarci wannan taron, sun amince cewa kyakkawan mulkin demokaradiya, da adilcin magabata, na samarwa matasa ayukan yi, tare da tsamo su daga fadawa ragar ‘yan ta'adda shi ne mafita.

Saurari cikakken rahoto daga Harouna Mamman Bako:

An Gudanar Da Taro Kan Matsalar Tabarbarewar Tarbiyya, Ta'addanci A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG