Masu Da'awar Jihadi Na Yin Zagon Kasa Ga Ilimin Boko A Jihar Tahoua Ta Nijar
Kamar yadda su ka yi ma sauran sassan rayuwa a Janhuriyar Nijar, masu da'awar jihadi na yin lahani ga bangaren ilimin boko a jihar Tahou.
Birnin Nkonni, Niger —
Ministan cikin gida da ke ziyara a wannan yankin ya yi alkawarin daukar matakai don a samu zaman lafiya.
A daidai lokacin da tawagar ministan cikin gida ta kammala rangadinta a kudu da ma arewacin jahar Tahoua, batun da ya taso da ma ya dauki hankulan jama'a shi ne yanda matsalar tsaro ta dabaibaye sha'anin karatun boko a arewacin jahar dake iyaka da kasar Mali, wadda ta kai ga rufe makarantu tare da samun kwararar dalibai zuwa wadansu yankuna domin samun damar yin karatun, kamar yanda ya ke faruwa a garuruwa irinsu Tebaram da sauransu, kamar yanda wadansu dalibai na wannan yankin suka bayyana wa sashen Hausa na VOA.
Duk da nuna damuwa babba a kan wannan lamarin, abin yafi karfin kananan hukumomi, inji Yahaya Maiyaki kansila a karamar hukumar Tebaram inda abin yafi kamari. Abin ya sa uwaye mata daukar magana a lokacin ziyarar Ministan na cikin gida a wannan yankin da ke iyaka da kasar Mali, inda suka koka, ta bakin Malama Safiya Gadoni game da wannan matsala ta rashin samun karatun boko wa yaran wannan yankin.
Biyo bayan ziyarar shugaban kasa a wannan yanki a watanin da suka gabata, hukumomin kasar sun kara dakaru a wannan iyakar, abin da ya sa kungiyar dalibai USN ta Tebaram, ta bakin magatakardanta, Aminu Abdullahi da ke iyaka da kasar Mali, yin kira ga gwamnati.
Malam Hamadu Adamu Suoley Ministan cikin gida, ya ziyarci garuruwa 12 na jahar Tahoua da ke fama da matsalolin tsaro, abin da ya bashi damar gani da idanu dama jin halin da jama'ar wadannan garuruwan suke ciki, inda ya bayyana wa manema labarai irin matakan da gwamnati ta dauka domin wanzar da zaman lafiya a wadannan garuruwan.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mammane Bako: