Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Morocco Ta Make Spain 3-0 A Gasar Cin Kofin Duniya


'Yan wasan Morocco
'Yan wasan Morocco

Kasar Morocco ta dan ceci nahiyar Afurka da duniyar Larabawa daga kunya, bayan da ta kasance daya tilo da ta rage a gumurzun kwallon kafa da ake gwabzawa a kasar Qatar.

Morocco ta lallasa Spain da 3 - 0 Kungiyoyin biyu sun shafe sama da mintuna 120 suna gumurzu, kamin aje bugun daga kai sai gola.
Morocco da ke kasancewa kasar Afurka daya tilo da ta rage a wannan gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar, ta cimma Kamaru wajen kai wannan mataki a 1990 a Italiya, sai da Ghana 2010 a Afurka ta Kudu kamin kuma Senegal a 2002 a Korea da Japan.
A jiya dai, kasar Brazil ta kai ga zagaye na gaba, bayan ta yi wa Korea ta Kudu gashin balbale 4 - 1.
Brazil za ta gamu da Croatia dake matsayin dan galadiman wassanin na kwallon kafa na duniya da suka wakana shekaru 4 da suka gabata a kasar Rasha.
Ana can ana dab da tashi a wasa mafi daukar hankali a karon 'yan 16, tsakanin Portugal da Switzerland, dalili ko shine ababe da dama da suka dabaibiye dan wasan kasar da tauraronsa ya soma dusashewa, cewa da Cristiano Ronaldo, a dauko da hira mai zafi da yayi a Piers Morgan ana dab da gasar kofin duniya, da korar sa da club din Man United yayi da yuwuwar komawarsa a club din Al-Nasser na Saudiya, da ma son ganin an ajiye a kan banci gabanin soma wasansu na yau da Switzerland da kashi 70% na yan Portugal ke bukata biyo bayan nuna bacin ransa da ya yi, bayan kocin Portugal ya fidda shi a wassan su na karshe na rukuni da kasar Koriya ta Kudu da ta lakume Portugal da ci 2 - 1 .
Hukumar kwallon kafa ta duniya ce FIFA, ta fito da sabon jadawalin matsayin kungiyoyin kwallon kafa na duniya kamar haka:
1- Brésil da maki 1828.
2- Argentine maki 1787.
3- Belgique maki 1781.
4- Angleterre da maki 1774.
5- France da maki 1770.
6- Pays-Bas da maki 1738.
7- Italie da maki 1724.
8- Espagne da maki 1693.
9- Portugal da maki 1679.
10- Croatie da maki 1666.
Sai dai kasashen nahiyar Africa na kusa na 20, dauko daga ta farko kasar Senegal:
1. Sénégal (18e a matsayin ta duniya)
2. Maroc (22e)
3. Tunisie (30e)
4. Nigeria (32e)
5. Algérie (37e)
6. Egypte (39e)
7. Cameroun (43e)
8. Mali (46e)
9. Côte d’Ivoire (48e)
10. Burkina Faso (54e)
Jamhuriyar Nijer ta yi kasa, inda take ta 121 da maki 1152 a jadawalin na FIFA.
Saurari cikakken rahoton Haruna Mammane Bako:
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:51 0:00
XS
SM
MD
LG