Rundunar 'yan sandar gundumar Birnin N'Konni a Jamhuriyar Nijar ta kama wasu gaggan masu safarar miyagun kwayoyi a yankin Afirka.
Rundunar a karkashin sashen ta na sarbike ce ta kama masu safarar miyagun kwayoyi daga Najeriya, Jamhuriyar Nijar da kan yi safarar kwayoyin zuwa kasashe 17 na yammacin nahiyar Africa da ma kasashen Maghreb zuwa Turai.
Shugaban gundumar Birni N'Konni malam Ralisu Aili, ya yabawa jami'an tsaron a game da wannan namijin kokarin da suka yi kana ya ce wannan zai taimaka wajen kare al'ummar.
Kazalika, shi ma shugaban rundumar 'yan sandan Konni, Kwamishina Suley ya yi farin ciki da wannan nasarar da ya bayyana cewar zai taimaka wajen magance matsalolin shaye-shaye kana wannan zai haifar da cigaba.
Jami'in tsaro Musa Bazuga, ya yi kira ga jama'a da su ba su goyon baya da ma ba su tabbacin ba su kariya da boye sunayensu.
An gudanar da wannan bikin gaban Magajin garin Birni N'Konni, da sarkin Birni N'Konni da Sarkin Fulanin Konni, da mataimakiyar Babban alkali mai shigar da kara a babbar kotun kasa ta Birni N'Konni da shugabanin rundonin tsaro na Birni N'Konni.