Zamu soma labarun wassanin mu na wannan makon da jamhuriyar Nijer, inda a karshen makon da ya gabata ne, hukumomin kasar, ta hanyar Ministan Wasannin Jamhuriyar Nijer, Seku Doro, suka yi wa kungiyar kwallon kafa ta yan wasa masu bugawa a cikin gida gagarumin marhabin.
Wannan ko ya biyo baya karkarewa a matsayi na 4 na kofin kwallon kafa na Nahiyar Africa da a ke cewa CHAN, da yan wasan na jamhuriyar Nijar suka yi a kasar Aljeriya.
Jamhuriyar Nijar dai, wannan shi ne karo na farko da ta ke kai wannan matsayin, inda ta kwashi sama da sefa million 300.
Idan ana tune, kasar Aljeriya mai masaukin baki, ta sha kashi a wassan karshe a hannun kasar Senegal a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan kungiyoyin 2 , sun share sama da minti 120 suna fafatawa.
A cigaba da wasan kwallon kafa ta duniya na kofin club – club zakaru a nahiyoyin su, a yau Talata, Flamengo ta gwabza da AL HILAL (2-3), yayin da a ranar gobe Laraba, Real de Madrid ke gogawa da AL AHLI.
A kasar Burtaniya, kungiyar kwallon kafa ta Man City, ke shirin sha babu dadi, da zaran wani kwamiti mai zaman kansa ya kammala bincike.
Abin ko ya shafi daruruwan keta haddi game da kashe kudade ba bisa ka’ida da a ke zargin kungiyar ta yi.
A dai shekara ta 2008, wani kamfani na hadaddiyar Daular Larabawa ya sayi club din na Man City kan kudi yuro million 260, kuma ya kuduri aniyar tabbatar da kungiyar a matsayin daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya.
Inda ko a 2021 – 2022, kungiyar ta kwallon kafa ta Man City, ta ci ribar yuro million 687
Yanzu dai abin kallo shi ne ko wane sakamako ne wannan kwmitin zai fito da shi ko kuma wane sirri ne zai bankado game da Man City?
A wasannin Tennis kuwa, yau 7 ga watan Fabrairun 2023, kusan shekara guda kenan da yar wasan Tennis yar kasar China, Peng Shuai ta yi batan dabo, bayan hirar da ta yi da mujallar kasar Faransa ta wasanni mai suna l’équipe
Daga bisani, yar wasar, ta yi kaukausar zargi ga wani kusan gwamnatin kasar China da ta ce yayi lalata da karfi da ita.
Kwamitin duniya na Tennis, ya ce yana magana da ita, amma har yanzu bai bayyana ina yar wasar take ba.
Shi ko kwamitin shirya wasannin tennis na duniya, ya ce har yanzu, bai samu damar yin gaba da gaba da yar wasan ba.
Saurari cikakken rahoton Harouna Bako: