N’KONNI, NIGER - A Jamhuiryra Nijar, an shiga daya daga cikin lokuta mafi hatsarin gaske, inda ake fuskantar arangama tsakanin manoma da makiyaya, lamarin da ke janyo asarar rayuka.
Wannan shi ya sa aka yi wata ganawa, tsakanin sarakunan gargajiya da suka samu wakiltar Sarkin Tahoua da gwamnan Jihar Tahoua da kungiyoyin manoma da makiyaya na Jihar domin tunkarar lamarin ganin cewa a wadansu yankunan na Jihar, kamar gundumar Keita, har an soma taho mugama tsakanin manoman da makiyaya da ya kai ga jikkatar wadansu daga cikin bangarorin guda biyu.
Magatakarda na kasa, daya daga cikin kungiyoyi na kasa na manoman ya ce dole ne sai an hadu an tattauna idan ana son a yi nasara wajen rigakafin wannan matsalar tsakanin manoma da makiyaya.
Tuni dai gwamnan Jihar ya umurci girka wata runduna ta hadaka ta jami'an tsaro a cikin kowace gunduma da niyyar tunkara duk wata husuma da ka iya tasowa a cikin jama'ar da ke zaune a wurin guda.
Saurari cikakken rahoto daga Haruna Mamane Bako: